Jagoran Lauyoyin da Ya jagoranci maka Ado Gwanja, Badamasi.S.Gandu a Kotu bayan Rera wakokin ASOSA da Chass Ya Magantu.

Spread the love

Biyo bayan umarnin da wata babbar kotun jahar Kano , ta bayar na kamo mata mawakin nan Ado Isah Gwanja, Barista Badamasi Sulaiman Gandu, ya bayyana cewar daman tun a shekarar 2023 da ta gabata suka shigar karar Ado Gwanja da kuma wasu mutane 8 , a gaban kotun shari’ar addinin musulinci dake Bichi, inda suka nemi kotun ta  bayar da umarnin ga kwmaishinan yan sandan jahar Kano ya kamo Ado Isah Gwanja da sauran mutane takwas din.

Barista Badamasi Gandu, ya ce tun a baya yan sanda sun kama Murja Ibrahim Kunya da kuma Ashiru Mai Wushirya har wata kotu a birnin Kano ta hukunta su bisa samunsu da aikata laifi.

Sai dai ya kara da cewa Ado Gwanja , ya garzaya gaban babbar kotun jahar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Justice Aisha Mahmud , domin dai ta hana jami’an yan sanda kama shi, kuma ya samu odar da ta hana kama shin din.

Barista Gandu ya kara cewa, kasancewar su ma su biyayya ne bin doka da oda ,sun bi umarnin kotun  har sai da ta yi hukuncin ta a ranar 26 ga watan fabarairun 2024.

Jagoran Lauyoyin da Ya jagoranci maka Ado Gwanja, Badamasi.S.Gandu a Kotu bayan Rera wakokin ASOSA da Chass Ya Magantu.

A gaggauta bude shagunan da ba a siyar da magani dake mai Karami Plaza Kano: Kotu

Babbar kotun jahar Kanon, ta saurari korafin mai kara da kuma wadanda aka yi kara wato yan sanda da bangaren lauyoyin , inda ta yi watsi da karar Ado Gwanja, tare da janye duk wani umarni da ta bayar abaya , sannan ta yi umarni ga jami’an yan sanda su kamo shi, kuma a ci gaba da gudanar da bincike akan wakokinsa da suka hadar da Chass da kuma Asosa.

Kotun ta ce kar ya kara yin wadannan wakoki a taron jam’a har sai an kammala bincike wanda hukumar tace fina-finai ta jahar jahar Kano da kuma jami’an yan sanda.

Sai dai rundunar ’yan sandan Jihar Kano, ta bayyana cewa har kawo yanzu ba ta samu wani umarni na kamo mawaƙi Ado Gwanja ba.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *