Gwamnatin Kano ta fitar da sabon umarni ga Sarakuna

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da mai martaba Sarkin Bichi daga yin sabbin nade-nade da kuma daga likkafar wasu hakimai a masarautar.

Idan za a iya tunawa masarautar ta Bichi ta shirya gudanar da nade-nade a ranar 1 ga watan maris 2024, Inda ta rubuta takardar neman sahallewar gwamnatin kano kafin aiwatar da nade-naden.

Bayanin dakatar da nade-naden na kunshe ne a cikin wata wasika da ta fito daga ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu ta jihar kano mai kwanan watan 21 ga watan Fabrairu 2024, mai dauke da sa hannun babban Sakataren ma’aikatar Ibrahim M Kabara.

A ranar larabar data gabata ma ma’aikatar kananan hukumomi ta sake fitar da wata sanarwar, Inda ta sanar da dukkanin masarautun jihar kano da su dakatar da duk wani shirinsu na yin nade-nande ko daga darajar hakimai.

Hukumar kwashe shara ta jahar Kano ta kaddamar da feshin maganin sauro a Unguwar Badawa

Hukumar kwashe shara ta jahar Kano ta kaddamar da feshin maganin sauro a Unguwar Badawa

Sanarwa ta ce ana umartar dukkanin masarautun jihar da su tabbatar suna sanar da Ofishin kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi da al’amuran masarautu ta jihar kano duk wani lamari da ya shafi irin wannan batun.

Wasu dai na ganin wannan Mataki ba zai rasa nasaba da kallon hadarin kaji da ake zaton akwai a tsakanin masarautun Kano, Bichi, Rano, Gaya da Karaye da kuma gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf ba.

KADAURA24

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *