Gwamnatin jahar Kano Ta Yi Alkawarin Kara Inganta Ilimin Yaya Mata Don Raba Su Da Yawon Tallace-tallace.

Spread the love

 

Gwamnatin jahar Kano, ta yi alkawarin kara inganta ilimin Yaya Mata a fadin jahar.

Kwamishinan ilimi na jahar Kano Hon. Umar Haruna Doguwa, ne ya bayyana hakan, a wajen taron da babbar mataimakiya ta musamman ga gwamnan jahar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, kan Ilimin Yaya Mata, Hon. Hafsat Aminu Adhama ta shirya wanda ya gudana a jami’a Yusuf Maitama Sule a ranar Asabar.

Doguwa ya Kara da cewa, gwamnatin jahar Kano ta sanya kaso mai tsoka cikin kasafin Kudi na shekarar 2024 domin kara inganta ilimin Yaya Mata a fadin jahar.

Kwamishinan Ilimi na Kano Umar Doguwa

Ya ce yanzu haka mutane da dama sun sanya hannayensu wajen taimaka wa harkar ilimin.

Gwamna Fintiri Ya Maka Dakataccen Kwamishinan INEC Na Adamawa, Hudu Ari A Kotu

Rashin isassun jami’an tsaro ne ke haifar da karuwar hare-hare a Kaduna – Uba Sani

Da ta ke yi wa Jaridar Idongari.ng, karin haske babbar maitaimaka wa gwamnan jahar Kano, kan ilimin Yaya Mata Hon. Hafsat Aminu Adhama, ta bayyana cewa sun shirya taron ne domin tara Dalibai Mata da Iyayensu don a wayar mu su da Kai, don su San muhimmancin iliminsu tare da kara zaburar da su wajen dage wa kan karatunsu.

SSA Hafsat Adhma

Hafsat Adhama ta Kara da cewa, za su kaddamar wani  shiri na Mayar da marayu Mata 500 Makaranta domin dakile su daga yawon tallace-tallace .

” Mun yi taro domin rabo wadannan yaran daga tituna , nan bada Jima wa ba” Hafsat Adhama “.

Adhma ta ce bayan sun kammala wannan aiki za su shiga kauyuka, don gabatar da taro na musamman da shugabanni da iyaye, Sarakuna da kuma Mallamai don su fahimci kudirinsu na kai Ya mace Makaranta maimakon ta kare a yawon Talla.

A cewar ta shirin nan na AGILE da ake bayar da tallafin Kudi duk Wata ga Dalibai matan, zai Samar da daidaito wajen Hana su zuwa talla, domin wa su idan an Hana su zuwa talla suna kafa hujjar cewar tallan shi ne yake rike su , amma za su yi kokarin wayar da su kan muhimmancin yin ilimi.

Sheik Mallam Ibrahim Khalil

Sheik Mallam Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa Ma ce tafi kowa tasiri a cikin al’umma , domin za su iya chanja Nigeria idan suka dage wajen sauya tunani da basu tarbiya mai kyau da kuma Ilimi.

Sai dai Mallam Ibrahim Khalil, ya Kara da cewa maimaikon a hana Mata yin amfani da shafukan sada zumunta, kamata ya yi a koyar da su hanyoyin da za su amfani da su wajen samun kudi ta hanyar kasuwanci .

” Idan aka koya wa Mata yadda za su yi amfani da shafukan sada zumunta ta hanyar kasuwanci da ilimi yafi a hana su yi”.

A kaeshe kwamishinan ilimin na jahar Kano, Umar Doguwa ya godewa Hafsat Adhama, bisa kokarin da ta keyi wajen karfafa wa mata gwiwa wajen neman Ilimi domin suma su yi fice a fannoni daban-daban.

Taron dai ya samu halattar Daliban Makarantu daban-daban a jahar Kano, Malamai , Matasa, yan siyasa , Iyaye , jami’an tsaro da dai sauransu.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *