Yan sandan jahar Adamawa da Mafarauta sun cafke wadanda ake zargi da garkuwa da mutane

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Adamawa, tare da hain gwiwar mafarauta sun samu nasarar kama wasu mutane biyu, wadanda ake nema ruwa a jallo, bisa zarginsu da aikata laifukan garkuwa da mutane.

Ana zamurgin tane biyu da yin garkuwa da Saddam Ahmadu da kuma Buba Adamu, har suka karbi kudin fansa naira Miliyan hudu da dubu dari bakwai (N4,700,000) a wajen yan uwansu.

Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jahar Adamawa SP Sulaiman Yahya Nguroje, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Makarantu a jihohi 14 na Najeriya na cikin haɗarin satar ɗalibai

Abdulsalami ya nemi Nijar, Mali, Burkina Faso su koma ECOWAS

SP Nguroje, ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da Ahmed Muhammad, mai shekaru 37 mazaunin karamar Song a jahar Adamawa da kuma Muhammed Haruna, mai shekaru 25 dan asalin jambutu dake karamar hukumar Yola ta Yamma.

Wannan nasarar na zuwa ne bayanan tattara bayanan sirri da dakarun yan sandan suka yi kan maboyarsu masu garkuwa da mutane, inda suka kwato bindiga kirar AK-47 da harsasai ma su rai 25.

Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa CP Dankombo Morris, ya yaba wa jami’an yan sandan da Mafarautan bisa nasarar da ake samu na kama batagarin.

Ya kuma bukace jami’an, su ci gaba da jajircewa don samun nasara, kuma ya bada tabbatacin cewar da zarar sun kammala gudanar da bincike za su gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *