Rundunar yan sandan jahar Kano ta musanta labarin da ake yada wa, kan wani mutum da ake zargin an Makure Wuyansa da Igiyar Kebir, akan Titin zuwa gidan gwamnatin jahar Kano.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce , ba gaskiya ba ne abunda ake yada wa, domin mutumin shi ya sanya kansa Kebir a wuya, kuma babu wani abu da aka kwata a wajensa.
A baya dai wasu da suke kusa da inda lamarin ya faru, sun yi zargin cewar wasu batagari ne suka makure wuyansa da Kebir har sai da suka tabbatar ya daina numfashi.
Kisan Ummita: Al’umma Na Dakon Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke Wa Frank Geng Quarong
Ana Son A Naɗa Betta Edu Sabon Muƙami A Gwamnatin Tinubu
SP Kiyawa ya Kara da cewa, bayan faruwar lamarin sun Kai mutumin asibiti , inda ya bayyana mu su gaskiya, da cewar shi ya sanya wa kansa Kabir sannan ya kwanta a wajen.
Jaridar Idongari.ng, ta ruwaito cewa rundunar yan sandan jahar Kano, bata yi cikakken bayani ba kan dalilin da sanya mutumin sanya wa kansa Kebir a wuya har sai da ya galabaita.
Yanzu haka dai yana ci gaba da asma tambayoyi a wajen jami’an yan sandan jahar Kano, don fadada bincike akansa.