Hukumar Hisbah A Kano Ta Cafke Gandaye 12.

Spread the love

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta samu nasarar kama wasu matasa 12 da ake zargin Gandaye ne, wadanda ba sa yin Azumi.

Hukumar Hisbar ta cafko matasan ne a wani sumame da ta kai a wuraren da suka hada da, Yankin Asibitin Murtala muhammed, Titin zuwa Kofar Wambai, Rrance Road, Igbo road, kasuwar Bata, Yankaba da kuma kasuwar Mallam Kato.

Ana zarginsu da yin kunnen kashi bayan an sanar da ganin sabon jinjirin watan Azumin Ramadan amma suka yin azumin a ranar farko.

Sai dai matasan sun bayyana cewar su a gidansu sai sunga watan da idanunsu biyu sannan suke daukar Azumin, sannan ba su san cewar anga watan ba sakamakon ba su da wayar salula ko radio .

Wasu daga cikin su sun hada da Danjumma ibrahim mai shekaru 20, mazaunin jahar Katsina, inda ya ce ya ci Rogo a cikin Kasuwa.

Yayin da wani mai suna Abdullahi Sulaiman mai shekaru 33, mazaunin Gezawa,ya bayyana cewar ya tashi da niyar yin Azumin amma ciwon Olsa ne yake damunsa shi yasa bai dauka ba.

Haka zalika akwai wani mai suna Lawan Ado Katsina, inda ya bayyana wa jami’an Hisbar cewar ya ci Rogo da kuma ruwa a kasuwar sabon gari Kano.

Mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisbah na jahar Kano DR. Mujahidin Aminuddin Abubakar, ya bayyana cewar ba za su daga wa Gandayen kafa ba, domin za su ci gaba da gudanar da sumame a lungu da sako na fadin jahar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *