Rundunar yan sandan jahar Kano, ta gurfanar da mutumin nan mai suna Umar Adam, dan shekaru 67, a gaban kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a Unguwar Gama Kano, bisa zargin da ake yi masa na yunkurin kashe kansa da kuma bayar da bayanan karya Wanda yin hakan ya Saba wa sashi na 119 da 297 na kundin SPCL.
Tunda fari ana zargin Umar Adam, da makure Wuyansa da wayar Kebir (Cable) a kusa da ofishin sakataren gwamnatin jahar Kano, tare da cewa wasu mutane ne suka kwace masa abun hawansa.
Sai dai cikin Wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta bayyana cewa, bayan faruwar lamarin sun yi gaggawar kai mutumin zuwa asibiti don kula da lafiyarsa.
Idan ba a manta ba jaridar Idongari.ng ta ruwaito mu ku cewa,wasu da suke kusa da inda lamarin ya faru, sun yi zargin cewar wasu batagari ne suka makure wuyansa da Kebir har sai da suka tabbatar ya daina numfashi.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce , ba gaskiya ba ne abunda ake yada wa, domin mutumin shi ya sanya kansa Kebir a wuya, kuma babu wani abu da aka kwata a wajensa.
Hukumar kwastam a Sokoto da Zamfara ta saki motoci 15 na hatsi da aka kama
Ku Maida Hankali Wajen Ilimin Yara Da Kula Da Tarbiyarsu Hon. Abubakar Jazuli Usman Gaya
Jaridar Idongari.ng, ta ruwaito cewa rundunar yan sandan jahar Kano, ta yi gudanar da zurzurfan bincike kan lamarin, bayan ya farfado, wanda ya shaida mu su cewar shida kansa ya sanya kansa kebir a wuya kuma ba a kwace masa komai ba.
Kan hakanne rundunar yan sandan ta gufanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da aikata laifuka biyu.
Mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala, ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa, nan ta ke ya amsa laifukan da ake zarginsa da aikatawa.
Sai dai ya shaidawa kotun cewar, ya yi hakanne sakamakon wahalhalu rayuwa na tsanani da rashin samun abinda zai ci, amma kodan babu wanda ya sanya masa Cable a wuya kuma babu abunda da aka karba a hannunsa sabanin abunda aka fada abaya.
Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ya sanya shi a hannun beli, amma sai shakikansa biyu sun yi alkawarin za su ci gaba da kula da shi, inda aka dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Afrilu 2024.