Karancin Ruwan Sha da na amfanin Yau da kullum ya sanya wata Ƙungiyar cigaban Al’umma ta “Society For Peace Development and Education” Karkashin Jagorancin Hon Auwal Abdullahi Yola da hadin gwiwar Gidauniyar Marigayi Ghali Na’abba ta fara raba ruwan Sha a sassan birnin Kano .
Da yake zantawa da manema labarai ya yin raba ruwan da aka gudanar a Unguwar Jakara a Karamar Hukumar birni. Hon Auwal Yolo ya ce sun bijiro da shirin ne duba da halin da Al’umma ke ciki na karancin ruwan Sha, tare da sassukaka mu su samun ruwan, musamman a wannan wata na Ramadan me Alfarmar.
Daga sai Hon Auwal Abdullahi Yola, ya ce Kungiyar da hadin gwiwar Gidauniyar za su Ci gaba da raba ruwan Shan , a sassan birnin Kano, dan samawa Al’umma sauki.
- Wata Sabuwa: Iyayen Abba Dan-Kuda Sun Tabbatar Cewa Yana Aikata Daba Da Shan Miyagun Kwayoyi
- Yan Sanda Sun Cafke Sojan Gona A Legas