Rundunar Yan Sandan Kano Ta Ce Za Ta Bi Umarnin Kotu Kan Rushe Masarautu

Spread the love

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta bayyana cewa, bayyana cewa za ta muntata umarnin da kotu bayar na Ranar 23 ga watan Mayu 2024 kan abinda ya shafi rushe masarautun Kano.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a shelkwatar rundunar dake Unguwar Bompai Kano.

CP Gumel, ya ce dukkan wani da ya yi yunkurin haifar da rudani , don kawo rashin zaman lafiya a jahar ba za su kyale shi, don Doka za ta yi aiki akansa.

A baya dai kotun ta bayar da umarnin Dakatar da rushe masarautun Kano har sai ta saurari karar da aka shigar da za ta saurara a Ranar 3 ga watan Yuni 2024.

Kwamishinan Yan Sandan ya Kara da cewa, ba su San da batun tura jami’an sojoji ba , gidan sarkin Kano dake unguwar Nasarawa, a matsayin sa na shugaban gamayyar hukumomin tsaron Kano.

Haka zalika ya ce kawo yanzu ba a ba su , takaddar kama tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero , a hukumance ba, amma sun gani sanarwar a shafukan sada zumunta.

Rundunar Yan Sandan tare da hadin gwiwar sauran hukumomin jahar sun ce , duk Wanda ya yi yunkurin kawo hargitsi za su Kama shi, don ya fuskanci hukunci.

Haka zalika gamayyar hukumomin tsaron sun ce za su a shirye suke don ci gaba da  tabbatar da Tsaro da kare rayukan al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *