Yan sandan Jigawa sun tabbatar da rasuwar mutane 11 a mummunan hatsarin mota.

Spread the love
CP AT Abdullahi

Rundunar yan sandan jahar Jigawa ta tabbatar da rasuwar mutane 11, sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da su a Kwanar Gujungu dake jahar.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Jigawa DSP Shiisu Lawan Adamu ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da aike da Idongari.ng, a ranar Asabar.

DSP Shiisu Adamu , ya kara da cewa, mummunan hatsarin ya ritsa ne da wasu mototoci guda biyu, Honda L.E. launin ruwan Toka mai Namba NSR 469 AE, inda wani mai suna Abdullahi Muhammad ya tuko ta dauke da fasinjoji 5 daga Kano da nufin zuwa Balangu, a karamar hukumar Kafin Hausa, sai kuma mota kirar Golf Wagon Ja mai numba AUY 292 XA , inda Direbanta mai suna Safiyu Mamu , ya dauko fasinjoji 4 daga Gujungu domin kai su karamar hukumar Taura.

A kan hanyar su ne mummunan hatsarin ya faru bayan sun yi karo da juna a kwanar Gujungu.

Bayan faruwar lamarin jami’an yan sanda suka kai wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibiti amma likita ya tabbatar da cewa dukkan mutanen dake cikin motocin biyu sun rasu.

Mutanen 11 da suka rasu sun hada da maza 5 da kuma mata 6 ciki harda kananan yara 2 .

Sunayen sun hada da Abdullahi Muhammad mai shekaru 35, mazaunin Tudun murtula,Samira Ahmad mai shekaru 45, Ummi Muhammad mai shekaru 36, Rabi Ahmad mai shekaru 35, Maryam Isah mai shekaru 32 da kuma A’isha Hamza mai shekara 1 dukkan su daga karamar hukumar Nasarawa ta jahar Kano.

Sauran sun hada da Safiyanu Mamu mai shekaru 40, Nura Muhammad mai shekaru 35 mazaunin Majia, Ikram Abdurrahid mai shekaru 3 mazauniyar Unguwar Yangayami , Lawal Mika’il mai shekaru 60 dake garin Gurjawa da kuma Abdurrahid Abubakar mai shekaru 35 daga Unguwar Yangayami duka a karamar hukumar Taura ta jahar Jigawa.

Kwamishinan yan sandan jahar Jigawa AT Abdullahi, a madadin jami’an yan sandan jahar , ya aike da sakon ta’aziyar sa ga iyalan mamatan da hatsarin motar ya ritsa da su, inda ya yi mu su addu’ar samun rahmar ubangiji da kuma fatan Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *