Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayyana cewa aiyukan daba a sassan birnin Kano ya kare sakamakon mika wuya da wasu makidan Gangi suka yi su 12.
Makida Gangi dai sune wadanda suke yi wa mafarauta kida don tsima su , ko kuma matasan da suke fito wa Fada don su kara tunzura su.
Kwamoshinan yan sandan ya ce makada Gangin sun ajiye Gangunan ne sakamakon yadda yan dabar ke tayar da hankulan jama’ar jahar.
Gumel ya kara da cewa, sunga babu wadanda za su kadawa Gangunan Ganginne yasa sukabar harkar baki daya.
” Na yi mu su marhabun lale, ya kuma yi mu su alkawarin cewar gwamnan jahar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, mutum ne mai son taimako da taisayi, inda ya tabbatar mu su cewar gwamnan zai samar mu su wuri a ma’aikatar raya Al’adu da tarihi ta jahar Kano don su dinga nishadantar da jama’a tare da biyansu wani kaso daga gwamnati har su manta da kidan Gangin ga Yan daba ko yan Tauri” CP Gumel”.
” Domin wannan kida ne na ziga har aje ayi abun da bai kamata ba , in sun zigasu sun aikata laifi sai su gudu” CP M.U. Gumel”.
Kwamishinan yan sandan ya ce wannan al’amari ya zame masa abun farin ciki, da cewar mutane sun amsa kiran da ake yi ganin cewar da gaske suke gudanar da aiyukan su.
Matasan makadan Gangin su 12 sun fito ne daga yankunan Kurna da Rijiyar Lemo wadanda a baya yankin ya fuskanci matsalar yan daba da dai sauransu.
Tun bayan zuwan kwamishinan yan sandan jahar Kano, a watan Mayun 2023 aka samu raguwar aikata laifuka musamman na fashin waya da sauran laifuka a jahar.
Yanzu haka dai al’ummar jahar na ci gaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum kamar yadda aka saba cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da dardar ba.