Hukumar saron Civil defence ta kasa reshen jihar Jigawa , ta cafke wani matashi mai suna Mika’ilu Abubakar , mai shekaru 27 mazaunin Unguwar ‘YanKoli a kauyen Zakirai dake karamar hukumar Kiyawa ta jahar, bisa zarginsa da aikata laifin Fyade ga karamar yarinya mai shekaru 8 a duniya.
Kakakin hukumar tsaron Civil Defence na jihar Jigawa ASC Badruddeen Tijjani Mahmud, ne ya bayyan hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis 10 ga watan Oktoba 2024.
Badruddin , ya ce sun sami korafi a ofishin su na garin Kiyawa ta hannun Yayan yarinyar da ake zargin an ci zarafin ta.
Rahotanni na cewa wanda ake zargin ya karbe Jarka yarinyar , har ta bishi zuwa gidansa don ta karba, amma ya aikata mummunar aika-aikar.
Binciken likitoci ya tabbatar da cewa an ci zarafin yarinyar tare ji mata ciwo.
Hukumar ta ce da zarar ta kammala gudanar da bincike za ta gurfanar da shi a gaban kotu don ya fuskanci hukunci.
- Kotun ɗaukaka ƙara ta jaddada dakatar da kasafin kuɗin da Gwamnan Rivers Fubara ya yi
- Jihohi 16 na neman Kotun Koli ta hana EFCC bincikar kudadensu