Yadda mazauna birnin Minna ke zanga-zangar tsadar rayuwa

Spread the love

Al’umma a Minna, babban birnin jihar Neja na gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Najeriya inda suka rufe manyan titunan da ke birnin.

Masu zanga-zangar sun hada da mata da matasa inda suke rera wakoki yayin da jami’an tsaro har da yan sanda ke gefe suna kallo.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito masu zanga-zangar na cewa tsadar kayan masarufi da rashin tabuka abin a zo a gani daga bangaren gwamnati wajen kawo sauki a lamarin ne ya tilasta musu rufe manyan tituna domin gwamnati ta ji kukansu.

Kotu ta buɗe asusun bankin Hukumar Hisba ta Kano

Mataimakin gwawamnan jihar Neja, Yakubu Garba a lokacin da yake yi wa masu zanga-zangar jawabi, ya ce gwamnati tana sane da irin kunci da wahalar da jama’a suke fuskanta a yanzu.

Ya ce gwamnati tana aiki domin rage halin matsi da aka shiga da kuma tasirin da ake gani sanadin cire tallafin mai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *