A Daina Kallon Fina-Finan Hausa Na Zamani — Jami’ar Danfodiyo

Spread the love

Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato ta yi kiran cewa akwai bukatar al’ummar kasar Hausa da su kaurace wa kallon fina-finan Hausa na wannan zamani.

Jami’ar ta yi wannan kira a yayin wani taron yini daya da masana suka shirya kan ina zamantakewar Hausawa ta dosa dangane da kallon fina-finan Hausa.

A bayanin da aka fitar wanda shugaban kwamitin taron, Farfesa Yakubu A. Gobir da shugaban Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Farfesa B.B Usman suka sanyawa hannu, sun ce masana sun bayar da shawarwari masu yawa kan batun da aka tattauna.

Aminiya ta ruwaito cewa masanan sun bayar da shawarwari guda biyar domin dawo da al’umma kan tsarin na al’ada mai kyau.

Masanan sun ce “akwai bukatar a rika shirya fina-finan Hausa wadanda suke nuna darussan kyawawan al’adun zamantakewar auren Hausawa na tarbiyya da kunya da biyayya tsakanin ma’aurata da ’ya’yansu kamar yadda wasannin kwaikwayo na da suka nuna.

Akwai bukatar magidanta da sauran al’ummar Hausawa su kauce wa kallon fina-finan Hausa na wannan zamani wadanda suka saba wa al’adu da addini da tarbiyar Hausawa, wannan zai rage yaduwar fina-finan da amfani da miyagun darussan da ke cikinsu.

“Al’ummar Hausawa [musamman matan aure] su guji dagewa da bata lokaci wajen kallon fina-finan Hausa da amfani da miyagun darussa da ke ciki na amfani da miyagun kalamai da saka sutura wadanda suka saba wa al’adun Hausawa da ke haddasa matsalolin rashin jituwa tsakanin ma’aurata da mutuwar aure barkatai.

“Ana ba da shawarar masana da manazarta su mayar da hankali sosai wajen rubutawa da shirya fina-finan Hausa masu koyar da kyawawan al’adu da dabi’un Hausawa. Saboda haka akwai bukatar gwamnati ta tallafa wajen daukar nauyin samar da irin wannan fina-finai da yada su.”

A karshen taron shugaban jami’ar, Farfesa Lawal Sulaiman Bilbis ya yi godiya ga mahalarta taron da wadanda suka bayar da gudunmuwa.

Farfesa Bilbis ya kuma alkawalin za a ci gaba da gudanar da irin wannan taron a gaba a kan al’amuran da suka shafi al’ummar Hausawa.

AMINIYA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *