Amintacciyar kungiyar Fulani ta Miyatti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) karkashin jagorancin Baba Othman Ngelzarma a madadin kafatanin jagororinta na kasa sunyi Allah wadai da irin kalaman kiyayya da wata kungiya mai suna( The International Group for Civil Liberties and Rule of Law) tayi kira ga Gwamnonin jihohin Kudu maso Gabas su guji baiwa makiyaya filayen kiwo.
Kungiyar miyatti Allah tayi Allah wadai da wannan kalamai na tunzura jama’a da kawo rashin fahimta da kungiyar () keyi a wannan lokaci.
Tabbas sanin kowa ne ga duk dan kasa mai son zaman lafiya ya zama wajibi ga masu neman hadin kai su rinka furta kalamai na wanzar da zaman lafiya ba na rarrabuwar kawuna ba..
Muna da kwarin gwiwar cewa Gwamnonin Kudu maso Gabas, tare da dukkan masu kishin kasa da kungiyoyi a yankin Igbo, za su ci gaba da gane ainihin mu, mu al’ummar fulani ba mu da wata manufa sai ganin an zauna lafiya da kawo cigaban kasa wannan shine manufar makiyaya yake a dukkan sassan Najeriya.
kuma za su ci gaba da yin adalci wajen karbar mutanenmu.
Hukumar Kwastan Ta Kama Muggan Kwayoyi Da Makamai A Tashan Jiragen Ruwa ta Legas
Ganin irin ƙwazon ƴan kabilar Ibo da irin nasarorin da suka samu a duk faɗin duniya (a wajen ƙasarsu ta asali), mun amince da yadda suke ci gaba da karɓar baƙi ga mutanenmu na ƙasar Igbo
Daga karshe mu Al’ummar Fulani makiyaya masu son zaman lafiya ne, muna kira gs dukkan yan kasa masu son zaman lafiya su cigaba da hada kai don mayar da Najeriya, uwa daya uba daya.
Sa hannu:
Bello Aliyu Gotomo
Sakatare na kasa MACBAN