A gaggauta bude shagunan da ba a siyar da magani dake mai Karami Plaza Kano: Kotu

Spread the love

Daga Mujahid Wada Kano.

Babbar kotun jahar Kano mai Lamba 4 karkashin jagorancin mai shari’a Usman Mallam Na’abba, ta bayar da umarnin bude shagunan da ba a sayar da magani, dake Namba 31/32 Niger Street, Mai Karami Plaza unguwar Sabon Gari Kano.

Wannan na zuwa ne bayan karar da Barista Nazifi Yusuf Gorondutse ESQ, ya shigar a madadin sauran ma su harkokin kasuwancin da bai shafi siyar da magani ba, da cewar an garkame mu su wuraren kasuwanci,  alhali kuma ba magani suke siyar ba.

Wadanda aka yi karar sun hada da Hukumar kula da magunguna ta kasa (Pharmacists council of Nigeria), Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) kwamishinan yan sandan jahar Kano (Commissioner of Police Kano Command )Hukumar Civil Defense (NSCDC).

Cikin Odar da kotun ta bayar ta ce wadanda aka yi karar su gaggauta bude ofisoshi da shagunan da ba sana’ar magani ake yi ba.
Akwai dai shaguna na masu saida Takalma da ofishin Lauyoyi da ma su siyar da wayar salula da dai sauransu.

Lauyan ma su kara Barista M.M. Bello ya shaida wa jaridar idongari.ng, cewar sun dauki wannan mataki sakamakon hana ma su karar damar shiga shagunan da suke harkokin kasuwancinsu, kuma ba magani suke siyar ba.

Idan ba a manata ba a ranar 16 ga watan fabarairun 2024, Idongari.ng, ta ruwaito mu ku cewar wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kanon ce ta umurci dillalan magunguna dake kasuwar kasuwar Sabon Gari a yankin Karamar Hukumar Fagge da su tashi nan ta ke.

Baya ga haka, kotun ta kuma ba da umarnin mayar da masu sana’ar ta hada-hadar magunguna zuwa cibiyar da aka kebe don siyar da magunguna a Dangoro da ke kan titin Zariya a Kano.

Ƴankasuwar Nijar sun yi watsi da ƙayyade farashin shinkafa

Gwamnan Gombe ya jinjina wa yarinyar da ta lashe gasar karatun Al-Ƙur’ani ta duniya

Alkalin Kotun Mai shari’a Simon Amobeda a hukuncin da ya yanke a ranar Juma’a 16/2/2024 , ya yi watsi da karar da kungiyar masu hada-hadar magunguna ta Najeriya, da wasu mutane shida suka shigar saboda rashin cancanta.

A ranar 17/2/2024, yan kasuwar sayar da Magani ta Sabongari Kano, sun rufe shagunan su, har sai abunda hali ya yi, biyo bayan hukuncin babbar kotun tarayya a jahar Kano, inda ta umarce su, su tashi su koma Kasuwar Dangoro a karamar hukumar Kumbotso.
Sai dai yan kasuwar sun bayyana rashin jin dadin su kan hukuncin kotun, da cewar sun shirya dauka kara, kan yunkurin raba su da sana’arsu.

Shugaban yan kasuwar Maganin ta jahar Kano, Musbahu Yahaya Khalid, ya bayyana cewa sun samu kwafin hukuncin kotun da cewar kotun ta kori kararsu, inda lauyoyinsu suka shirya tsaf domin daukaka kara.

Tuni dai hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC reshen Jihar Kano tare da hadin gwiwar Hukumar da ke Kula da Magunguna ta Kasa sun rufe shagunan magani 1321 da ke Malam Kato da Mai Kari Plaza da kuma cikin Kasuwar Sabon Gari a jihar.

Shugaban Hukumar a Jihar Kano, Kashm Ibrahim ya ce, sun rufe shagunan ne don ganin masu maganin sun bi doka ta hanyar komawa Kasuwar Dangwauro wacce Gwamnatin Jihar ta tanadar musu.

Haka kuma, Kashin Ibrahim ya ce za a ci gaba da samar da wasu shagunan a cikin kasuwar don magance matsalar da ‘yan maganin ke dogaro da ita cewa rashin isassun shagunan ne ya hana su komawa kasuwar.

Kotun karkashin jagorancin Usman Na’abba, ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Maris 2024.

Idongari.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *