Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya ce saɓaninsa da tsohon gwamnan jihar, bai wuce saboda ƙarfin ikon jan ragamar jihar ba.
Fubara ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da tashar talabijin na Channels a ranar Talata, a lokacin da yake bayyana rikicin da ya dabaibaye siyasar jihar, inda bayan zaɓen ƙananan hukumomi aka wayi gari da rigima.
A game da alaƙarsa da Wike, Fubara ya ce, “gaskiya ba zan so in wannan maganar ba a nan, amma duk waɗanda suka san abin da ke faruwa, sun san cewa a kan ƙarfin ikon jan ragamar mulki ne.
Misali tunda an gudanar da zaɓe a Rivers na ƙananan hukumomi, kuma an rantsar da su, shin me zai sa wani ya hana su shiga ofis? “Wataƙila saboda akwai wani wanda yake tunanin ya fi ƙarfin jihar.”
A game da yarjejeniyar maslahar da suka yi a baya, Fubara ya ce, “babu wata yarjejeniya da na karya. Ya dai kamata kowa ya ajiye kari.
Shi kansa ogana minista ya kamata ya sani bai kamata a lalata jihar Rivers ba. Yayi gwamnan jihar, wani ne yake kai yanzu, wanda yake kai yanzu goyon baya yake buƙata saboda bayan shekara huɗu ko takwas nima zan tafi, wani ya ci gaba.
“Idan lokacin zaɓe ne, za ka iya fafatawa, amma bayan an gama zaɓe, an fara mulki, goyon baya ake buƙata.”