A Matsayin Na Lauyoyi Yan Jaridu Abokan Aikin Mu Ne: Dr. Nuhu Musa I.

Spread the love

 

Wani masanin shari’a daga tsangayar koyar da shari’a a jami’ar Bayero Kano, Dr. Nuhu Musa Idris, yaja hankalin yan jaridu, su dinga gudanar da aiyukansu daidai da doka, da kuma fahimctar bangarorin gwamnati kafin su isar da sakonsu ga al’umma.

Barister. Dr. Nuhu, ne ya bayyana haka a wajen taron karawa juna sani na yini daya, da cibiyar ci gaban al’umma da wayar da kai, Citizen for Development and Education ( CDE) ta shiryawa yan jaridu a jahar Kano.

Lauyan ya ce wajibi ne yan jaridu su san yadda ake amfani da kalmomin kotu ko kuma fassara su, domin akwai wasu daga cikin yan jarida da basa fadinsu daidai ko fassara su daidai.
” A wannan zama mun yi kokari mun gabatar da jawabai yadda za a fahimci yadda kalmomin suke”Dr. Nuhu M”.

Ya kuma kara da cewa a matsayinsu na lauyoyi yan jaridu abokan aikinsu ne, saboda a bangare daya suka yi tarayya wajen hidimtawa al’umma duk da cewar yadda suke gudanar da aiyukansu ya bambanta.

” mu muna kallon su a wani ginshikin gwamnati, saboda duk wani tsari da ake da shi, bangaren zartarwa, shari’a da kuma majalissa babu wanda yasan me suke yi, inda ta hannun yan jarida ba”cewar masanin shari’ar, Dr. Nuhu Musa”.

Ya kuma yi fatan dukkan dan jarida zai kasance mai aikata daidai ba rashin daidai ba, domin idan bai bi a hankali ba zai iya fadawa wajen da yake ganin daidai zai yi kuma ba daidai zai yi ba.
” kuma dole an bi an kiyaye kamar yadda doka ta fada tun daga makaranta nasan an koyar da yan jaridu yadda za su bi doka, kuma shirya irin wannan taron bana son ya zama shi ne karshe , ya kamata a rinka yin sa akai-akai don samun karin haske”.

A karshe Lauyan ya ce a matsayin na dalibin ilimin shari’a har yanzu bai ga wata doka da ta bayar da mar daukar fuskar wanda ake zargi da aikata wani laifi ba,dake hannun hukumomin tsaro.

” za a iya zargin mutum a kaishi gaban jami’an tsaro su bincika su ga bai da laifi su sallame shi, kuma an dauki hotonnan na shi ya riga ya zama abu da ya watsu kuma ba za a bi mutane ace kowa ya goge wannan hoto ba, to ni dai ina neman wannan fatawa ga su jami’an tsaro ko kuma wasu masana da suka fini da malamaina a sanar da mu mukaru saboda mukara fadawa mutane ko akwai amma ni dai a yanzu bansan wata doka da ta ba da dama a haska mutumin da ake tuhuma ba” DR. Nuhu Musa’.

Babban jami’in Cibiyar ci gaban al’umma da wayar da kai, Citizen for Development and Education ( CDE) , Ambasada Ibrahim Waiya, ya ce dole sai yan jaridar sun zabura wajen neman ilimi don sanin yadda za su bunkasa aiyukansu ta hanyar ilimi da sanin doka da kuma sauran al’amura.

SARARI MURYAR DR NUHU MUSA IDRIS

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *