Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya, ta buƙaci a gaggauta janye ƙarin farashin man fetir a ƙasar.
Ƙungiyar ta buƙaci shugaba Bola Tinubu ”ya umarci kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya gaggauta soke ƙarin farashin man da yayi, wanda shi ne karo na biyu a cikin wata ɗaya, har zuwa lokacin da za a samu hukuncin kotu a kan ƙarar da aka shigar domin ƙalubalantar ƙarfin ikon kamfanin NNPCL game da ƙara farashin mai a ƙasar.”
A watan da ya gabata, ƙungiyar SERAP ta shigar da ƙara, inda take neman kotu ta tilastawa shugaba Tinubu da kamfanin NNPCL ”mayar da farashin man fetir a yadda ya ke kafin ƙarin, da kuma neman a gudanar da bincike a kan almundahanar da ake zargin ana tafkawa a kamfanin NNPCL.”
- KANO STATE POLICE COMMAND EMBARKS ON ROBUST SECURITY SENSITIZATION
- Yan Sanda Sun Gurfanar Da Matasa Dauke Da Takaddun Tuhuma 20 Bisa Zargin Satar Dabbobi A Kano
Mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya ce “Sabon ƙarin farashin man fetir ɗin a daidai lokacin da ake gaban kotu domin tantance ƙarfin ikon masu alhakin ƙara farashin, cin fuska ne ga tafarkin shari’a”
SERAP ta buƙaci shugaba Tinubu ya gaggauta bayar da umarnin dakatar da sabon farashin man har zuwa lokacin da kotu ta yanke hukunci a game da ruɗanin da aka shiga na neman tantanci wanda ke da ƙarfin ikon ƙara farashin mai a Najeriya.