A rufe duka layukan da ba haɗa da NIN ba – NCC

Spread the love

Hukumar sadarwa ta Najeriya, NCC ta sake jaddata umarninta ga kamfanonin sadarwar na ƙasar da su rufe duka layukan wayar da ba a haɗa su da lambar katin ɗa ƙasa ta NIN ba.

Daraktan yaɗa labaran hukumar, Mista Reuben Mouka, ne ya bayyana umarnin a lokacin wani taron kasuwanci da aka gudanar a Kaduna.

Mista Mouka ya ce dole ne masu amfani da layin waya su haɗa shi da lambar katin ɗan ƙasarsu ta NIN.

Ya ce an ɗauki matakin ne don magance matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta.

Yan Sandan Kano sun cafko mutum na 2 da ake zargi da laifin garkuwa da kuma kisan kai

Har Yanzu Ba A Ba Mu Umarnin Kamo Ado Gwanja Ba — SP Abdullahi H. Kiyawa

Mista Mouka ya jaddada wa’adin yau Laraba, 28 ga watan Fabrairu da aka bai wa kamfanonin sadarwar su rufe duka layukan da ba a haɗa da lambar NIN ba.

Dama dai hukumar NCC ta ɗaɗe tana kiran al’ummar ƙasar da su haɗa lambar wayarsu da ta katin ɗan ƙasarsu wato NIN, a wani mataki na daƙile ayyukan matsalar tsaro a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *