Abba ya yi tafiya yayin da rikici ya dabaibaye NNPP a Kano

Spread the love

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi tafiya zuwa Abuja, yayin da rikici ke ƙara tsamari a jami’yyar NNPP a jihar.

A ranar Litinin, gwamnan ya yi sasanci tsakanin Sakataren Gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi, da wasu wakilan mazaɓarsa da suka nuna rashin jin daɗinsu kan yadda abubuwa ke tafiya.

Duk da sasancin gwamnan, jam’iyyar ta dakatar da Bichi da Kwamishinan Sufuri, Muhammad Diggol, bisa zargin rashin biyayya ga jam’iyyar.

Gwamnan ya yi jiran kusan sa’o’i biyu a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano, kafin daga bisani ya tashi zuwa Abuja.

A lokacin da gwamnan ya yi tafiya, jagoran jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na ganawa jiga-jigan jam’iyyar jihar.

Ko da aka tambayi Kwankwaso kan rikicin NNPP, ya ƙi yin tsokaci, inda ya ce shugabannin jam’iyyar sun ɗauki matakin da ya dace.

A baya-bayan nan dai wasu sun nuna damuwa kan irin ikon da Kwankwaso ke da shi a siyasar gwamnatin Kano, wanda suke ganin hakan yana hana Gwamna Yusuf gudanar da ayyukasa yadda ya kamata.

Hakan ne ya sa wasu ƙungiyoyi fara kiran da “Abba Tsaya da Kafarka”, a wani yunkuri na raba Gwamna Yusuf da Kwankwaso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *