Abin da ministan kuɗin Najeriya ya ce kan zanga-zangar NLC

Spread the love

Ministan kuɗi a Najeriya, Wale Edun ya ce gwamnati ta ɗauki wasu manyan matakan sauye-sauye a tattalin arzikin ƙasar da ya kamata a ce tuntuni an yi su waɗanda ya ce yanzu da aka yi ana jin raɗaɗin hakan.

Ministan yana magana ne game da zanga-zangar yini biyu da ƙungiyar ƙwadago ta kira yau da kuma gobe Laraba domin nuna takaici kan yadda al’umma ke fama da tsadar rayuwa a Najeriya.

Yanzu haka tashin farashin kayan masarufi a ƙasar ya kai kimanin kashi 30 cikin 100 yayin da darajar takardar naira ke ci gaba da zubewa.

Matsalar ƙarancin lantarki na ƙara dagula al’amura.

Bankin ci gaban ƙasashen nahiyar Afirka ya yi gargaɗin cewa za a iya fuskantar tashin hankali a ƙasar saboda yunwa.

Ministan ya faɗa wa BBC cewa “Shugaba Bola Tinubu ya duƙufa wajen cika alƙawurran da ya ɗaukar wa ƴan Najeriya na cewa ba za a bar talakawa da masu rauni a baya ba.”

Ya ce “saƙona shi ne na sake jaddada abin da shugaban ƙasa ya ce, cewa sauye-sauyen nan sun zama dole kuma yana jin raɗaɗin sannan yana ƙoƙari na ganin ya rage shi tare da taimaka wa waɗanda suka fi fuskantar matsi kuma yana ɗora ƙasar kan turbar farfaɗo da tattalin arziki kuma ya buƙaci mutane su ƙara haƙuri a wannan lokacin sannan yana yin duk mai yiwuwa na rage raɗaɗi da taƙaita lokacin da hakan zai ɗauka.”

Kwastam ta tabbatar da mutuwar mutane a turmutsitsin raba shinkafa

Yan sandan Kano sun gurfanar da mutane 9 Kan zargin sayar da Dala ba bisa ka’ida ba.

Ministan ya bayyana cewa abin da gwamnati ke son yi shi ne samar da isasshen abinci da samun isassun kayan da ake nomawa a ƙasar.

Ya bayyana cewa tashin dalar ya faru ne sakamakon hauhawa kuma a cewarsa, gwamnati ta yi ɗamara na rage hauhawar farashin kayayyaki.

Ya ƙara da cewa idan har masu zanga-zanga suka tunkare shi, zai nemi su bai wa sauye-sauyen lokaci domin su yi aiki.

Najeriya na tsaka da halin matsin rayuwa inda farashi ke tashin gwauron zabi da kashi 30 cikin 100 a shekara yayin da darajar naira ke ƙara raguwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *