Abin da sabuwar dokar sarakuna masu daraja ta biyu a Kano ta ƙunsa

Spread the love

Kwana ɗaya bayan hukuncin wata babbar kotun jiha da ta umarci sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu da dokar masarautun Kano ta 2020 ta kafa da su daina ayyana kansu a matsayin sarakai, ƴan majalisar jihar ta Kano sun sake amincewa da wata sabuwar dokar da ta ƙirƙiri sabuwar masarautar Kano da ta ƙunshi sarki mai daraja ta ɗaya guda ɗaya da masu daraja ta biyu guda uku.

  • Masarautar Kano: Masarautar Kano ita ce mai daraja ta ɗaya, inda sauran sarakuna masu daraja ta biyu za su zama ƙarƙashin ikon sarkin Kano mai daraja ta ɗaya. Masarautar mai daraja ta ɗaya na da iko na kai tsaye da hakiman ƙananan hukumomi 36 daga cikin 44 na jihar.
  • Masarautar Rano: Sarki mai daraja ta biyu na wannan masarauta na da ƙananan hukumomi uku wato Rano da Bunkure da Kibiya.
  • Masarautar Ƙaraye: Ita kuma wannan masarautar mai daraja ta biyu ta ƙunshi ƙananan hukumomi guda biyu na Ƙaraye da Rogo.
  • Masarautar Gaya: Ita ma wannan masarautar mai daraja ta biyu ta ƙunshi ƙananan hukumomi uku na Gaya da Ajingi da kuma Albasu.

Abin da dokar ta tanada

Wannan doka wadda take gaban gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf domin jiran sanya mata hannu ta zama cikakkiyar doka kamar yadda majalisa ta tabbatar wa BBC, ta tanadi abubuwa kamar haka:

  • Sarakuna guda uku masu daraja ta biyu za su rinƙa karɓar dukkan wani umarni kai tsaye daga sarkin Kano mai daraja ta ɗaya.
  • Masarautun za su rinƙa gudanar da dukkan wasu naɗe-naɗe da ayyukansu bisa sahhalewar gwamnan jiha ta hannun kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautun gargajiya.
  • Dokar ta bai wa gwamna dama a cikin ƙanƙanin lokaci ya naɗa duk wanda ya ga cancantarsa a matsayin sarki mai daraja ta biyu a gundumomin guda uku, kafin a fitar da tanadi dangane da hanyoyin da za a bi wajen naɗin sarakan a nan gaba bisa dalilan gado ko mutuwa ko murabus. Za kuma a fitar da tsarin hanyoyin gudanarwa ga masarautun a nan gaba.

Da zarar gwamnan Kano ya sanya mata hannu za ta zamo cikakkiyar doka, sannan kuma gwamna Abba Kabir Yusuf zai naɗa da bayar da sanda ga sabbin sarakan masarautun masu daraja ta biyu guda uku bisa shawarar sarki mai daraja ta ɗaya.

Shari’o’i kan rikicin sarautar Kano

A ranar Litinin, 15 ga watan Yuli ne mai shari’a Amina Aliyu ta babbar kotun jihar Kano ta umarci sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu na Rano, Ƙaraye, Bichi da Gaya da su daina ayyana kansu a matsayin sarakai.

Kotun ta kuma umarci sarakunan biyar da su miƙa duk wasu kaya na sarauta mallakar masarauta ga gwamnatin jiha.

Majalisar dokokin jihar Kano ce dai ta shigar da Aminu Ado Bayero da ƴan sanda da sojoji a gaban kotun.

To sai dai kuma kafin hukuncin na ranar Litinin, babbar kotun tarayya da ke zaman ta a jihar Kano ta yanke hukuncin cewa dokar da ta rushe masarautu a jihar na nan daram amma kuma ta soke aiwatar da dokar wadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

A lokacin yanke hukuncin, Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya ce ba daidai ba ne gwamnan jihar Kano ya aiwatar da dokar soke masarautun saboda akwai umurnin kotun da aka bayar da ya dakatar da duk wani yunƙuri na gwamnan Kano wajen aiwatar da sabuwar dokar da ta cire rawanin sarakuna biyar a jihar ta Kano.

Mai shari’a Liman ya ce “A don haka na bayar da umurnin cewa dukkan matakan da gwamnati ta ɗauka na soke su amma hakan bai shafi sabuwar dokar masarautu ba. Amma sun shafi matakan da gwamna ya dauka ciki har da sanya hannu a sabuwar doka da kuma sake nada Sanusi”.

Kotun ta ce “An soke dukkan matakan da masu kare kai a shari’ar suka ɗauka, amma kuma hakan bai shafi dokar ba.”

Bisa dokar ne dai gwamna Abba Kabir Yusuf ya rushe sarakunan biyar ciki har da Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki na 16, bayan da tsohon gwaman jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe shi a 2020.

A ranar 23 ga watan na Mayu ne ɗaya daga cikin masu naɗa sarkin Kano, Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya ƙalubalanci dokar a babbar kotun tarayyar da ke Kano, inda ya nemi alƙalin da ya rushe dokar a matsayin haramtacciya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *