Abin da ya janyo tsaikon biyan maniyyatan Abuja kuɗin guzurinsu

Spread the love

Gaba a yau ne hukumar jin dadin alhazai ta Najeriya, reshen Abuja ta ce za ta ci gaba da aikin biyan maniyyatanta 2,958 da ke Saudiyya cikon kudin guzurinsu na dala 200.

Tun farko aikin ya gamu da cikas bayan da wasu daga cikin maniyyatan suka yi barazanar dukan jami’an da suka je raba kuɗaɗen tare da nuna rashin amincewarsu da cikon dala 200 a maimakon dala 300 da tun farko aka sanar za a cika masu lokacin jigilarsu zuwa kasa mai tsarki.

Mataimaki na musamman ga ƙaramar ministar Abuja shawara, Dr Abdullahi Isa Kauranmata wanda ya kira taron gaggawa domin tattauna ƙalubalen da maniyyatan babban birnin ke fuskanta, ya ce suna ƙoƙari domin ganin an sauƙaƙa wa maniyyata tare da inganta walwalarsu a ƙasa mai tsarki.

Ya ce “na ji korafinku game da kuɗin guziri kuma na nemi a fara biyanku kuɗaɗenku, amma abin mamaki sai na ji wasu na barazanar dukan jami’an da suka zo”.

Dakta Kauranmata ya bayyana cewa duka maniyyatan da aka ba su dala 500, gwamnatocin jihohinsu ne suka tallafa masu.

Ya ce sauyin da aka samu ya faru ne sakamakon hauhawar da dala take yi duk da cewa an sanar da kowane maniyyaci cewa za a bashi cikon dala 300.

A ranar Asabar ne dai wasu maniyyatan Abujan suka yi ƙorafin cewa hukumar alhazan birnin ta saɓa alƙawarin da ta yi musu na ba su kuɗin guzuri, bayan da hukumar ta ce ba za ta basu dala 300 da ta yi musu alƙawari tun da farko ba.

Dakta Kauranmata ya kuma yi alƙawarin nema wa maniyyatan sauki daga ministan babban birnin domin rage masu radadin da suke fuskanta.

Ya kuma yi magana kan matsalar jinkirin da maniyyata ke fuskanta inda ya yi alƙawarin za a samar da ma’aikatan lafiya da za su riƙa bai wa maniyyata marasa lafiya kulawa domin shirya wa babbar ibadar da ke tafe ta sauke aikin hajji.

Game da ƙorafin abinci da maniyyata ke yi, Dakta Kauranmata ya ce zai kai ziyara zuwa wurin da ake dafa abincin domin gani da ido da nufin cimma matsaya kan irin abincin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *