Majalisar Dattijan Najeriya ta ce halin da aikin ‘yan sanda ke ciki a kasar na buƙatar a zauna a sake masa fasali.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Mataimakin shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin ya ce ba a gina hukumar ‘yan sandan Najeriyar kan yadda za ta yi nasara ba.
Sanata Ahmed Abdulhamid Malam-Madori wanda shi ne shugaban kwamitin aikin ‘yan sanda na Majalisar dattijan ƙasar, ya shaida wa BBC cewa tabbas batun haka yake, saboda yadda ake da ƙwararrun ƴansanda a ƙasar da za su iya fitar da ita a idon duniya, sai dai aikinsu na cikin gida babu inganci.
”Mu na da ƙwararrun ƴansanda da suka goge a fannin aiki, kuma ko ina muka shiga da su ba za mu ji kunya ba, amma ƙarancin samun kuɗi na gudanarwa da rashin kyautata wuraren ba su horo da lalacewar makarantun ƴansanda sun lalace idan aka kwatanta da na baya.
Sanata Ahmed Malam-Madori ya ce dole a kyautata wuraren da ake bai wa ƴansanda horo, a kuma haɓɓaka aikin ƴansanda ta hanyar ƙara musu kuɗaɗe wajen kasafin kuɗi, da inganta wuraren horonsu da duk wani abu na kyautatawa gare su.
Ya ƙara da cewa “yadda ake gudanar da kasafin kuɗi ta ɓangaren ƴansanda abin bai taka kara ya karya ba, hatta a kasafin kudin bana ba a bai wa wurin fifiko ba,Inda ya ce ya kamata yadda ake bai wa sojin sama da na ƙasa da na ruwa kuɗi su ma ƴansanda indai ba a ba su sama da na sojoji ba, to bai kamata a ba su ƙasa da haka ba, saboda idan ana batun tsaro ƴansanda ne a sahun gaba domin sojoji ba wannan horon aka ba su ba.”
Sanata Ahmed Abdulhamid Malam Madori ya ce akwai ƙudurori kan batun inganta aikin ƴansanda da ƴan majalisa za su gabatar a zauren majalisar, za kuma su yi ƙokarin ganin an tabbatar da su.
”A ciki akwai batun gyaran makantun ƴansanda da suka lalace, akwai batun fansho saboda ƴansanda na karbar mafi ƙanƙantar fansho, saboda abin da ake bai wa sojoji ya ninka wanda ake bai wa ƴansanda, lamarin akwai tausayawa a ciki.”
An jima ana sukar gwamnatin Najeriya kan batun na inganta aikin ƴansanda, da albashi mai tsoka da muhalli da walwalarsu, abin da ake ganin na taka rawa wajen ta’azzara cin hanci da rashawar da ake zargin wasu ƴansanda da aikatawa.