A jihar Kano, har yanzu tsugune ba ta ƙare ba, duk da kammala zaɓen ƙananan hukumomi tare da rantsar da sabbin shugabannin, saboda rikicin shari’a.
Hukumar zaɓen Kano ta ce jam’iyyar NNPP ce ta lashe duk shugannin ƙananan hukumomi 44 da kansiloli 484, to sai dai har yanzu ba a rantsar da shugaban karamar hukumar Kumbotso ba.
Ɗaya daga cikin ƴan takarar kujerar ne ya garzaya babbar kotun jihar saboda sauya sunansa da wani, abin da ya sa kotu ta yi hukuncin da ake ganin shi ne ya hana rantsar da sabon shugaban.
Ana gobe zaben shugabannin ƙananan hukumomi a Kano wato ranar 25 ga watan nan na Oktoba ne wata babbar kotun jiha ta yi hukunci, bayan Ali Musa Ɗanmaliki na jam’iyyar NNPP ya kai ƙarar jam’iyyar da kuma hukumar zaɓen jihar, gaban babbar kotun jihar saboda sauya sunansa da Abdullahi Ghali Shitu a matsayin wanda zai yi takarar.
Kuma bayan kotu ta saurari kowanne ɓangare ne, sai ta yi hukuncin da ya warware duk wani sauyi da aka yi tare da tabbatar da shi Ali Musa Ɗanmaliki a matsayin ɗan takara.
Kuma a haka aka shiga zaɓen ana jani-in-jaka tsakanin mutanen biyu, sannan bayan an sanar da sakamako aka rantsar da shugabanin ba tare da rantsar da na Kumbotso ba.
Tuni dai bangaren Abdullahi Ghali Shitu wadda shi ne jam’iyyar NNPP tace ta tsayar suka ɗaukaka ƙara game da hukuncin babbar kotun.
Ranar 31 ga wannan watan da muke ciki ne ɓangaren da ake ƙarar za su koma kotun don a saurari roƙonsu na a jingine hukuncin.