Abin da ya sa ban saka dokar taƙaita zirga-zirga a Kaduna ba’

Spread the love

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce bai yi tunanin sanya dokar taƙaita zirga-zira a jihar ba, saboda wasu dalilai.

Yayin da yake zantawa da BBC Hausa, Gwamna Uba Sani ya ce mutanen da suka fita zanga-zanga a jihar tun ƙarfe 3:00 na rana suka tashi.

”Shi ya sa ni ban taɓa tunanin sanya wata dokar taƙaita zirga-zirga ba, saboda hakan zai cutar da wasu da dama a jihar”.

”Idan ka sanya dokar, kana nufin duk wani ɗan kasuwa, ya rufe kasuwancinsa, to kuma ka san nawa ake asara?

”Akwai fa wanda sai ya ce ya buɗe kasuwa a ranar sannan ya samu abin da za a ci a gidansa a wannan ranar”, in ji gwamnan.

Gwamnan ya kuma ce bai ji daɗini yadda wasu mutane suka yi ta ɓarna a wasu yankunan arewacin ƙasar ba.

Ya ƙara da cewa rashin fitar waɗanda suka kira zanga-zangar ne ya haifar da tashin hankali a wasu jihohin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *