Gwamnan jihar Katisna Mallam Dikko Umar Radda ya buƙaci Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya yi masa bayanin dalilin rashin halartar wasu hakiman masarautarsa bikin hawan sallah da aka gudanar a masarautar.
Kwamishinan yaɗa labarai da al’adun gargajiya na jihar, Dakta Bala Salisu Zango ya tabbatar wa BBC cewa ba wata gagarumar matsala aka samu tsakanin gwamna da sarkin ba, face kawai batu ne na neman bahasi kan gazawar wasu hakimai wajen halartar hawan sallah duk da shirin da aka yi tun farko.
”Gwamnanmu mutum ne mai sha’awar abubuwan da suka shafi al’adun gargajiya, kuma Katsina jiha ce da ta yi fice a ɓangaren hawa na sarakuna, kamar lokacin bukukuwan Sallah da Sallar Gani, to da lokacin sallah ya ƙarato sai gwamna ya nemi yadda za a inganta hawan Sallah a masarautar, aka ba shi shawarar tallafa wa masarautun da kuɗi da kuma goyon bayan gwamnati, amma duk da goyon bayan da gwamnati ta bai wa hakiman, wasu ba su fito hawan Sallar ba, wannan shi ne dalilin da ya sa gwamna ya nemi jin bahasi”, in ji kwamishinan yaɗa labaran.
A cikin kwanakin nan ne wata takarda da gwamnan ya aika wa mai martaba sarkin Katsina ta karade shafukan sada zumunta.
Takardar ta bukaci mai martaba sarkin Katsina Abdulmumini Kabir ya yi bayani kan abin da ya sa wasu hakimai suka ki halaryar hawan sallah a birnin Katsina.
A lokacin da ya yi wa BBC karin bayani, kwamishinan yaɗa labaran jihar Katsina ya ce gwamnati ta riga ta zauna da sarakunan jihar biyu (Na Daura da na Katsina) gabanin hawan sallah, saboda yadda za ta taimaka musu wajen gudanar da hawan sallar, amma sai wasu hakimai ba su fito ba, don haka gwamnati tana da damar jin dalilin rashin fitowarsu.
”Kamar kai ne a ka bayar da aiki, kuma sai ba a yi maka ba, to mene ne aibu idan ka nemi jin bahasin dalilin rashin yi maka aikin?”
Kwamishinan ya tabbatar da cewa babu wata matsala tsakanin gwamnatin jihar da masarautar Katsina.
Wannan tuhuma dai ta haifar da shakku da fargaba a zukatan mutanen jihar waɗanda ke zargin cewa gwamnan na shirin fasalta masarautar domin sauke wasu hakiman tare da musanya su da wasu da ke kusanci da ita.
To sai dai kwamishinan ya ce babu ƙanshin gaskiya game da zargin, yana mai cewa ”wannan tunanin mutane ne, kuma ba za ka hana mutane faɗin abin da ke bakunansu ba”.
Ya ƙara da cewa su masarautun gargajiya a ƙarƙashin ikon gwamnatin jiha suke a kowace jiha, kuma gwamna na da madar yin duk abin da ya ga dama kan masarautun.
”Babu inda gwamnatin Katsina ta ce za ta fasa wata masarauta a jihar nan, amma kuma wannan ba yana nufin gwamnati ba ta da ikon da za ta yi hakan ba”, in ji kwamishinan.
”Iko ne na gwamna ya yi yadda yake so bisa daidai a jiharsa, muddin zai yi wa al’ummar jiharsa daɗi”, in ji shi.
”Masarauntun gargajiya a ƙarƙashin ikon gwamna suke a kowace jiha, kuma duk abin da gwamna yake ganin zai yi wa al’ummarsa daɗi to fa zai yi shi, amma dai gwamnatin Katsina ba ta taɓa cewa za ta fasa wata masarauta a jihar Katsina ba”.
Rikici tsakanin sarakuna da gwamnoni dai wani abu ne da ke neman zama ruwa dare musamman a wasu yankunan arewacin Najeriya.
Ko a baya-baya nan ma an ga yadda ake ta kai ruwa rana a Kano kan batun masarautun jihar bayan da gwaman jihar Abba Kabir ya sauke sarakunan jihar tare da naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon sarkin Kanon, bayan gyaran dokar masarautu da majalisar dokokin jihar ta yi.
Haka a makon da ya gabata, gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya aike da ƙudurin gyaran dokar masarautu gaban majalisar dokokin jihar domin yi mata gyaran fuska, wani abu da wasu ke ganin tamkar rage wa Sarki Musulmi ƙarfin iko ne.
Masu sharhi dai na ganin cewa galibi abin da ke janyo samun saɓani tsakanin sarakunan gargajiya da gwamnonin jihohi, shi ne zargin rashin nuna goyon baya ga jam’iyyun gwamnonin a lokacin yaƙin neman ba.
To amma kwamishinan yaɗa labaran ya ce a jihar Katsina babu wannan matsalar, domin a cewarsa sakarunan Daura da na Katsina ba su tsunduma kansu harkokin siyasar jihar ba.
”Sarakunan jiharmu biyu na Daura da na Katsina sun ja girmansu, sun kare mutuncinsu ba su shiga harkokin siyasa ba”, in ji shi.