Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce gwamnoni ba su da iko na bai wa rundunonin tsaro umarni kai tsaye a jihohinsu duk da cewa kundin tsarin mulki ya bai wa gwamnonin cikakken iko kan jihohin nasu.
Janar Christopher Musa ya bayyana haka ne a wani bangare na taron yini biyu kan matsalar taɓarɓarewar tsaro, wadda ta ki ci ta ki cinyewa a arewacin Najeriya.
Gamayyar kungiyoyin farar-hula da ke arewacin Najeriya ce ta shirya taron da za a kammala ranar Alhamis, inda aka gayyato dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da mataimakin shugaban kasar da gwamnoni da ministoci da sarakunan gargajiya da kuma kwararru da nufin samar da mafita.
Janar Christopher Musa ya ce akwai dalilai da dama da suka sa hakan saboda ana tafiyar da lamuran tsaro ne daga wuri guda inda ya kara da cewa “idan mun ce za mu bar kowa ya rika magana, ba ka san abin da ke cikin zuciyarsa ba.”
Ya ce idan an samu afkuwar wata matsala ta tsaro, “shi gwamna yana iya magana da kwamanda cewa ga matsalar da ake gani, shi ya san matakin da ya kamata ya dauka.”
A cewar sa, ba zai yiwu su bai wa gwamna umarni irin wanda za su bai wa sojoji ba saboda a kan haka ake aiki kuma suna sane da duk abubuwan da ke faruwa game da tsaro.
Rashin ba mu iko kan tsaro na kawo cikas – Gwamnoni
A baya-bayan nan dai ana samun koke-koke daga wani ɓangaren al’umma kan cewa ya kamata gwamnoni su taka rawa a harkar tsaro fiye da wadda suke takawa a yanzu.
Su kansu gwamnonina lokuta da dama sun koka kan rashin ba su ƙarfin iko a lamurran tsaro.
Ko a lokacin taron, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce iyakance masu iko kan batun tsaro na kawo cikas a kokarinsu na bayar da gudummawa ta fuskar tsaro.
A cewarsa, “kundin tsarin mulkin Najeriya bai bai wa gwamnoni dama da za su yi hoɓɓasa ta tsaro ba, sai dai kame-kame da ake yi wanda shi ma an kalubalance shi – batun kawo jami’an ko-ta-kwana.”
Sojoji sun kuɓutar da mutum uku da akayi garkuwa da su a jihar Taraba
Hedikwatar tsaron Najeriya ta gargadi kungiyar HURIWA kan rikicin Filato
Lamarin ya sanya wasu daga cikin gwamnonin suka yanke shawarar fito da ƙungiyoyin ƴansintiri, waɗanda suke taimakawa wajen lura da yadda al’amura ke gudana a yankunansu.
Sai dai gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce akwai bukatar a sake nazarin wasu dokokin kasar saboda a cewar sa, babu jiha ɗaya tilo da za ta iya bugar kirji don maganin matsalar tsaro.
“Dole gwamnatoci na jiha da tarayya da yan majalisa sai sun saka hannu, akwai al’amuran da ba za su iya yiwuwa ba sai majalisa ta duba kundin tsarin mulkin kasar nan an masa kwaskwarima.” in ji gwamnan na Kaduna.
Shi ma tsohon shugaban Najeriya, Abdussalami Abubakar ya ce matukar ana son a kawo maslahar tsaro a Najeriya musamman a yankin Arewa, dole ne a hada karfi da karfe domin samun nasara.
“Tsaro fa ba aikin soja ko dan sanda ko masu kayan sarki ne kawai ba, kowannen mu – mace da namiji da yaro da babba yana da taimako da zai iya yi cikin wannan matsala da muke fama da ita,”
“Masu kawo mana wannan fitina a cikinmu suke, ya kamata mu tashi tsaye muga mun yi maganinsu mun ba da shawarwari ta yadda za a samu maslaha.” in ji tsohon shugaban kasar.