Abin da ya sa muka kori Seaman Abbas daga aiki – Rundunar soji

Spread the love

Rundunar tsaro ta kasa a Najeriya, ta yi ƙarin bayani game da dalilan sallamar sojan ruwan nan Seaman Abbas Haruna daga aiki.

A wajen wani taron manema labarai da ta kira a Abuja, hedikwatar tsaron ta ce an sallami Seaman Abbas daga aiki ne bayan wata kotun soji ta same shi da wasu laifuka uku da ake zarginsa da aikatawa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaron ta Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya shaida wa BBC cewa, Seaman Abbas, ya yi wasu abubuwa na rashin ɗa’a.

Tukur Gusau, ya ce kwamandan bataliyar da wannan soja ke aiki ya kasance yana magana da sojojinsa, to sai shi Seaman Abbas ya fara surutu da kuma wasu abubuwa na rashin ɗa’a, to sakamakon haka sai kwamandan ya ce mishi ya kai kansa wani ɗaki da ake tsare mutane idan sun yi laifi, to sai yaƙi zuwa.

“Daga nan ne sai kwamandan ya ce tun da yaƙi zuwa to a karɓe bindigar dake hannunsa, to maimakon ya miƙa bindigar sai ya fara harbe-harbe har sai da fitar da harsashi 16, to Allah ya kiyayye bai harbi kowa ba”.

Tukur Gusau, ya ce a ɓangaren aikin soja ba a wasa da batun bindiga ko harsashi, domin harsashi ɗaya idan soja ya fitar sai an bibiya an ga me yasa ka fitar da shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaron ta Najeriya, ya ce, “Bisa ga wannan aka tuhumeshi inda aka tura shi kotun soja kuma koda aka kai shi ya amsa laifinsa, a kan haka ne kotu ta tuhumeshi da aikata laifuka uku”.

Ya ce a watan Fabrairun 2023, kotun ta kore shi daga aiki.

Tukur Gusau, ya kuma bayyana cewa a ka’idarsu ta aikin soja dole sai an ɗauki wannan hukunci na kotu an kai wa manyan shugabannin sojin wanda kuma suke yanke hukunci na karshe wato wajen amincewa ko akasin haka da hukuncin kotu.

Kuma kafin shugabannin soji su yanke hukunci na karshe sai sun nemi ƙarin bayani daga manyan lauyoyi na rundunar sojin da mai laifi ke aiki.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaron ta Najeriya, ya ce, Da farko sai da Seaman Abbas ya nuna kamar bashi da lafiya, don haka sai da yaje asibiti da dama don a tabbatar da cewa ba’ayi masa shari’a a cikin yanayi na rashin lafiya ba.

Kuma kodayake asibitocin sun tabbatar da cewa lafiyarsa ƙalau, sannan ne kuma aka yi masa shari’a.

Kimanin shekaru biyar kenan da aka tuhumi sojan ruwan wato Seaman Abbas Haruna, da aikata wasu laifuka a lokacin da aka tura shi aiki a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya.

An dai tabka zazzafar mahawar a shafukan sada zumunta na Najeriya game da zargin cin zarafi da kuma azabtar da sojan ruwan bayan da matarsa ta bayyana cewa an ɗaure shi tsawon shekara shida cikin mummunar yanayi har ya samu taɓin hankali.

A cikin wani faifan bidiyo matar Abbas Haruna, ta bayyana cewa an gana masa uƙubar da ta wuce misali.

Matar mai suna Hussaina ta bayyana ne a wani shiri na gidan talabijin na ‘Brekete Family’, inda a ciki ta bayyana wasu zarge-zargen cewa ba a yi wa mijinta da ma su iyalansa ɗin adalci ba.

Bidiyon na Hussaina ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka riƙa yaɗa shi, wasu na zagi, wasu na Allah wadai, wasu kuma suna cewa a dai yi bincike.

Seaman Abbas Haruna dai ya kwashe shekaru 12 yana aikin soji kamar yadda mai ɗakin nasa Hussaina ta bayyana cewa “yana cikin sojojin ruwa na 21AK” abin da ke nufin ya fara aikin ne a shekarar 2012.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *