Abin da ya sa na bayar da gudummowar likkafani da tukwane – Sanata Hanga

Spread the love

Sanatan da ke wakiltar mazaɓar Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Rufa’i Sani Hanga ya yi ƙarin haske kan tallafin likkafani da tukwanen ƙasa da ya yi wa al’ummar mazaɓarsa.

Cikin tattaunawarsa da BBC, Sanata Hanga ya ce abin da ya yi sadaka ce kasancewar hatta likkafanin ma yana yi wa jama’a wahala idan aka yi mutuwa.

“Abin da ya ja hankalina shi ne, za a yi mutuwa a unguwa a zo ana neman likkafi a rasa, sai an yi karo-karo kafin a samu kuɗin sayen likkafanin, saboda talaucin da ake ciki a unguwanar”, in ji sanatan

Ya kuma ce dama a gidansu an saba bayar da gudunmowar irin waɗanna abubuwa, irin su ƙasar burji domin toshe ƙaburbura.

Sanatan ya ƙara da cewa ”Sai na ga yanzu yadda ake cikin wannan hali na matsin rayuwa, sai na yi tunanin cewa a baya ma ana wahalar likkafani, ina ga yanzu, sadaka ce ba wai aikin mazaɓa ba ne”.

Al’amarin dai ya janyo zazzafar muhawara a tsakanin al’umma da ‘yan siyasa musamman a shafukan sada zumunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *