Abu biyar da muke so masu zanga-zanga su gabatar mana kafin fara ta – ‘Yansanda

Spread the love

Yayin da wasu ‘yan Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa ranar 1 ga watan Agusta, rundunar ‘yan sandan ƙasar ta buƙaci masu shiga zanga-zangar su gabatar mata da sunaye da cikakkun bayanansu.

Babban Sifeton ‘yansandan ƙasar, Koyode Egbetokun ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja bababn birnin ƙasar.

Ya ƙara da cewa duk ƙungiyoyin da ke da muradin shiga zanga-zangar su gabatar da sunaye da cikakkun bayanansu ga kwamishinonin ‘yansandan jihohin da suke.

Mista Egbetokun ya ce rundunar ta ɗauki matakin ne don tabbatar da an yi zanga-zangar cikin kwanciyar hankali da lumana.

“Za mu tabbatar da ‘yancin da kundin tsarin mulki ya bai wa ‘yan Najeriya na taruwa don gudanar da zanga-zangar lumana,” in ji shi.

“Domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, muna kira ga duka ƙungiyoyin da ke sha’awar shiga zanga-zangar, su gabatar da cikakkun bayanansu da kwamishinonin ‘yansandan jihohin da za su yi zanga-zangar”.

Bayanan da Babban Sifeton ‘Yansandan ya buƙaci masu son shiga zanga-zangar su gabatar sun haɗa da:

  • Wurin da za su taru da hanyoyin da za su bi.
  • Lokacin da suke tunanin za su ɗauka suna yi
  • Sunaye da lambobin wayar jagororin da suka shirya zanga-zangar.
  • Matakan hana shigar ɓata-gari cikin zanga-zangar.
  • Gano waɗanda za su iya tayar da fitana a lokacinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *