Abu shida da za ku yi don kauce wa bugun zuciya a lokacin kallon wasan ƙarshe a gasar Afcon

Spread the love

Ma’aikatar lafiya ta jihar Legas ta buƙaci mazauna jihar su rungumi wasu shawarwarin kula da lafiyarsu a yayin kallon wasan ƙarshe na gasar Afcon da Najeriya za ta kara da Ivory Coast.

Hukumar ta bayar da shawarwarin ne domin kaucewa samun matsalar lafiya daga masu kallo a lokacin kallon wasan.

Aƙalla mutum uku ne dai rahotoni suka ce sun mutu a lokacin da suke kallon wasan da tawagar Super Eagles ta kara ta Afirka ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe, sakamakon bugun zuciya.

Gwamnatin jihar Kaduna ta dauki nauyin nuna wasan Najeriya a wasu wurare

Rundunar yan sandan Kano ta shirya tsaf don bayar da cikakken tsaro a ziyarar Uwar gidan shugaban kasa Oluremi Tinubu.

Cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiyar jihar Legas ya fitar, ya zayyana wasu shawarwari shida da ya ce mutane su yi ƙoƙarin kiyayewa a lokacin da suke kallon wasan, don kauce wa samun matsala.

Shawarwarin sun haɗar da:

1. Ka san matsayin zuciyarka: Yana da kyau ka son iya abin da zuciyarka za ta iya jurewa. Ka yi ƙoƙarin tuntuɓar likita domin sanin wannan, sannan ka yi ƙoƙarin kauce wa duk abin da zai sa ka ƙetare iya abin da zuciyarka za ta iya jurewa.

2. Yawaita shan ruwa da cin lafiyayyen abinci: Ku kauce wa shiga taron cunkoson da ba a samun wadatacciyar iska, domin samun ingantacciyar iskar numfashi, sannan ku kauce wa yawaita shan basara, tare da tabbatar da shan ruwa mai yawa da lafiyayyen abinci, domin samun wadataccen ruwa a jikinku, musamman la’akari da tsawon lokacin da za a ɗauka a zaune ana kallon wasan.

3. Yawaita miƙewa domin hutu: Ku yawaita tashi tsaye, kuna miƙe jikinku, inda hali ma a riƙa ɗan zagayawa don kauce wa gajiya da bai wa hanyoyin jini damar kewaya jini.

4. Zama da kyau ba tare da taƙura ba: Yana da kyau ku samun wurin zama mai kyau ta yadda ba za ku takura ba. Hakan na rage yawan gajiya da ciwon gaɓoɓi.

5. Kwantar da hankali da nutsuwa: Yana da kyau ku riƙa gwada abubuwan da za su sanya ku nutsuwa kamar riƙe numfashi, da ƙoƙarin danne damuwa da ɓoye fushi a tsawon lokacin da za a ɗauke ana wasan.

6. Shiryawa buƙatar gaggawa: Yana da kyau ku kalli wasan a wuraren da ke kusa da jami’an lafiya da wuraren da ke da hanyoyin kulawar gaggawa.

Daga ƙarshe hukumar lafiyar ta shawarci su tuntuɓi asibiti da zarar sun ji wasu alamun da ba su gamsu da su ba a lokacin da suke kallon wasan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *