Sabon shugaban riko na kungiyar daliban Hausa a kwalejin ilmi ta Aminu Kano, AKCOE, hadin gwiwa da jami’ar tarayya da ke Dustin-ma a jihar Katsina FUDMA kuma na farko a tarihin makarantar, kwamared Abubakar Sabo, ya ba da tabbacin yin aiki tukuru, tare da dukkannin shugabannin kungiyar, domin samar da duk wani ci gaba wajen tafiyar da kungiyar.
Ya kuma nemi hadin kan sauran wadanda suka nemi takara amma ba su sami nasara ba, dama ragowar daliban makarantar na sashin Hausa, da su ba da hadin kai wajan cigaban kungiyar domin ciyar da ita gaba, da Kuma ganin kara bunkasar harshen na Hausa a fadin Duniya.
A jawaban su daban-daban shugaban kwamitin samar da kungiyar tare tabbatuwar shugabannin rikon, Dakta Magaji Ahmad Gaya, da sakataren sa malam Ahmad Mikha’il sun ja hankalin sabbin shugabannin rikon da su zama masu juriya da hakuri tare da gaskiya da rikon Amana don samar da ci gaban kungiyar wajan ganin ta je duk in da ya kamata ta je.
An dai nada Abubakar Sabo, a matsayin shugaba sai Rabi Ahmad mataimakiyar shugaba, da Abdulmusawwir a matsayin magatakarda da sauran mutane goma sha biyu, amukamai daban-daban.