ABUBAKAR SABO YA SABA LAYAR RANTSUWA A MATAYIN SABON ZABABBEN SHUGABAN KUNGIYAR HAUSA NA KWALEJIN ILMI TA AMINU KANO (AKCOE) HADIN GWIWA DA JAMI’AR TARAYYA DA KE DUTSIN-MA A JIHAR KATSINA.

Spread the love

 

Sabon zababben shugaban kungiyar daliban Hausa na kwalejin ilmi ta Aminu Kano (AKCOE) hadin gwiwa da jami’ar tarayya da ke Dutsin-ma a jihar Katsina (FUDMA) kwamared Abubakar Sabo, ya ce, zai hada kai da duk masu son ganin harshen Hausa ya cigaba da bunkasa, a ko ina su ke, don kai wa ga gaci.

 

Kwamared sabon ya bayyana hakan ne, jim kadan kadan da rantsar da shi da sauran shugabannin kungiyar a wannan rana.

 

Anasa jawabin shugaban kwalejin dakta Ayuba Ahmad wanda ya sami wakilcin daraktan da ke kula da shirye-shiryen makarantar dakta Dalladi Abdu bukata ya yi ga sabbin shugabannin kungiyar da za su zama jakadu na gari a duk in da suka sami Kan su.

A jawaban su daban-daban daraktan da ke kula sashin dalibai a kwalejin wato Dean students affairs dakta Ibrahim Muhammad da kuma shugaban sashin Hausa da dakta Mahe Isah Ahmad Jan hankalin sabbin shugabannin su ka yi da su kasanace masu hakuri da juriiya da kuma riko da gaskiya da Amana.

 

Al’umma da dama me suka sami halattar taron bikin kaddamarwar ciki har da sakataren kungiyar ‘yan jarida na jihar Kano kwamared Abubakar Shehu Kwaru. Da shugaban kungiyar daliban makarantar kwamarrd Najub Kabir.

 

Cikin wadanda aka kaddamar akwai Rabi Ahmad Abubakar a matsayin mataimakiyar shugaba da Murja Murtala Muktar ma’aji da sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *