Kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta sanya ranar 3 ga watan Fabarairun 2024, domin gudanar da zaben cike gurbi, a wasu daga cikin jahohin Nijeriya da aka samu matsaloli yayin gudanar da zaben watan Maris na shekarar da ta gabata ta 2023, ciki harda jahar Kano.
To sai dai an samu matsaloli a wasu guraren gudanar da zaben na ranar Asabar 3 ga watan Fabarairun 2024, musamman, inda yan daba suka hana zabe da yunkurin farwa ma’aikatan zaben.
ABINDA TAWAGAWAR JAMI’AN TSARO TA GANI A HANYAR KUNCHI.
Tunda sanyin safiya ranar Asabar din, rundunar yan sandan jahar Kano, hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro , sun cafke wasu yan dabar siyasa kusan 70, akan hanyar karamar hukumar Kunchi ta jahar, dauke makamai da suka hada da da Gorori, kayan maye, wukake da daidai sauransu.
Yan dabar dai sun taho akan wata mota kirar Kanta, wadanda ake zargin sun tsaya domin tare ma’aikatan zaben da sauran al’umma don aikata barna.
Da yake ziyar gani da ido kan yadda zaben ke gudana, kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel , ya bada umarni gudanar da bincike kan matasan yan dabar, da suka samu kan hanyar dauke da makamai har ya bayar da umarnin gudanar da bincike.
Jagoran yan dabar siyasar da ake zargi mai suna Abdurrazak Muhammad wanda akafi sani da ( Mai salati Tukuntawa) , ya bayyana cewar , dan takarar kujerar majalissar dokokin jahar Kano, Ya’u Gwarmai ne ya dauko su tare da basu naira dubu goma-goma.
Abdul’aziz ya kara da cewa ya taho da matasan daga unguwannin, Farawa, Darmanawa, Tukuntawa da kuma Hausawar Gidan Zoo.
To sai dai dan takarar majalissar dokokin jahar Kano a Kunchi da Tsanyawa, Hon. Ya’u Gwarmai, ya bayyana cewa shi bai turo kowa ba, domin tayar da hankulan al’umma kamar yadda matasan yan dabar suka bayyana wa jami’an tsaro kawai sun yi hakan ne domin bata masa suna.
Kano: INEC ta dakatar da zaben karamar hukumar Kunchi, bayan yan daba sun gudu da kayan zabe
An ɗaure ƴar fim saboda yin liƙin kuɗi lokacin biki
Anasa jawabin kwamshinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayyana cewar, Matasan yan dabar da aka cafke sun bayyana mu su cewar daya daga cikin dan takarar majalissar dokokin jahar Kano, mai suna Ya’u Gwarmai ne, ya gayyato su domin su aikata ba daidai ba.
CP Gumel ya kara da cewa, za su yi kokarin samun Gwarmai din domin tabbatar da dalilinsa na tara irin wadannan matasa domin suje su tayar da hankulan al’umma.
” a yanzu mun gansu da gorori , kuma a daji wanda muna zargi hakika kamar suna shirin farwa ma’aikatan zabe da sauran al’umma bayan an kammala zaben” CP Gumel”.
Kwamishinan yan sandan ya ce sun fara gudanar da bincike, kuma sun karbe dukkan makaman dake wajen su.
YADDA YAN DABAR SIYASAR SUKA HANA GUDANAR DA ZABEN A KUNCHI.
Hukumar zabe mai zaman kanta, ta kasa INEC ta dakatar da zaben cike gibin a karamar hukumar Kunchi ta jahar Kano, biyo bayan tarwatsa kayan zaben da yunkurin farwa jami’an INEC daga wasu fusatattun dabar siyasa.
Kwamishinan zaben jahar Kano, Ambasado Abdu Zango, ya bayyana wa Idongari.ng, cewar, yan dabar sun kwashe kayan zaben,a karamar hukumar Kunchi, inda sukaje da gamayyar hukumomin tsaro , don tseratar da lafiyar ma’aikatan zaben.
Ya kara da cewa sauran kananan hukumomi biyar da suka hada da , Tsanyawa, Rimin Gado, Tofa, Kura, Garin Mallam, an gudanar da zaben, in banda kunchi da aka matasalar da ta janyo dakatar da zaben.
” An yi zabe a kananan hukumomi biyar cikin shida, amma a Kunchi ba mu samu abunda yakamata ba, domin yan ta’adda da kuma mutanen da basu da kishi sun watsa zaben tare da kwashe kayan zaben” Ambasada Abdu Zango”.
MARTANIN HUKUMOMIN TSARO A KANO.
Kwamishinan yan sandan Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayyana cewa yanzu haka jami’an tsaro sunanan a yankin domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.
” Zan godewa al’ummar jahar Kano musamman guraren da aka yi wannan zabe, har aka tattara sakamakon zaben cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya”.
Sai dai kwamishinan yan sandan, ya ce abunda ya faru a karamar hukumar Kunchi, kowa ya sani cewa gari ne a lungu ba akan hanya ba kuma ba kwaryar birnin Kano ba, inda suka lura cewar mutane sun dauki alkibilar , asaka, a raka, a tsare, kuma yan dabar sun tsoratar da mutane da ma’aikatan INEC tare da kwashe kayan zaben.
” kamar yadda kwamishinan zaben Kano ya bayyana maka , hukumar zaben ta kasa ta soke wannan zabe na karamar hukumar Kunchi, saboda rashin zaman lafiya” CP Gumel”.
CP Gumel ya kara da cewa yanzu haka akwai jami’an tsaro sama da 200, da suke gudanar da sintiri don kar wani abu ya taba ofishin hukumar zaben dake yankin.
A karshe ya yi kira ga masu irin wannan hali da su dinga sassautawa domin daukar Adduna, Gora, Wukake , ba al’adace mai kyau ba.