Ƙungiyar tuntuɓa ta dattawan arewa wato Arewa Consultative Forum ta ce ta dakatar da shugaban majalisar ƙolinta, Mamman Mike Osuman dangane da wasu kalamai da aka alaƙanta da shugaban a wani taronta da ta yi ranar Laraba a Kaduna.
A wata sanarwa mai sa hannun Alhaji Bashir Muhammad da Alhaji Murtala Aliyu, ƙungiyar tuntuɓa ta musanta wasu bayanai da ke yawo cewa sun bayyana goyon bayan fito da ɗantakarar shugaban ƙasar Najeriya daga yankin arewa a 2027.
Ƙungiyar ta kuma ce yankin na arewa na fama da ƙangin talauci da matsalar tsaro da jahilci, inda ta bayyana cewa gundarin matsalar yankin na hannun ‘yan arewa.
Ƙungiyar ta bayyana cewa an jirkita bayanan ta wata fuskar da ba ita ce alƙiblar da ta ɗauka ba, haka ma ta nuna damuwa game da yadda yankin na arewa ya samu kansa a komabaya, a fannonin da suka shafi ilmi da tattalin arzki da kuma talauci, sai kuma uwa-uba matsalar tsaro.
Wannan na kumshe ne a cikin wata takardar bayan taro da kakakinta Farfesa Tukur Baba ya sakawa hannu a ranar Laraba, da kuma aka raba wa manema labarai.
Wadannan kalaman na zuwa ne bayan da aka samu wasu bayanai da wasu jaridun Najeriya suka wallafa da ke cin karo da juna da aka danganta da shugaban kungiyar tuntuba ta dattawan arewacin Najeriyar, Mamman Mike Osuman, da aka ce ya fadi cewa lokaci ya yi da yankin ya dace ya fito da shugaban da zai jagoranci Najeriya a shekarar 2027, da kuma ya san zafin al’ummarsa.
BBCH