Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na tawagar Super Eagles ta Najeriya da ƙungiyar Atalanta ta Italiya, Ademola Lookman ya lashe kyautar ɗan ƙwallon ƙafa na Afirka.
Ɗan wasan ya doke fitattun zaratan ƴan wasa irin Achraf Hakimi na Morocco da Simon Adingra na tawagar Ivory Coast da ƙungiyar Brighton & Hove Albion ta Ingila da Ruto Williams na Afirka ta Kudu da Serhou Guirassy na ƙasar Guinea da ƙungiyar Dortmund ta Jamus domin lashe kyautar.
An gudanar da bikin karrama gwarazan ƴanwasan na Afrika ne a a birnin Marrakech na ƙasar Morocco
Lashe kyautar a wannan karon ya sa ƴan wasan Najeriya biyu sun lashe kyautar sau biyu a jere bayan Victor Osimhen da ya lashe kyautar a bara.
Wane ne Ademola Lookman?
Asalin sunansa shi ne Ademola Olajade Alade Aylola Lookman, kuma an haife shi ne a ranar 20 ga watan Oktoban 1997 a Wandsworth da ke ƙasar Ingila.
Ya wakilci tawagar ƙasar Ingila a matakin ƴan ƙasa da shekara 19 da ƴan ƙasa da shekara 21, kafin daga bisani ya zaɓi ya koma Najeriya domin ya wakilci babbar tawagar ƙasar ta Super Eagles, wadda ita ce ƙasarsa ta asali, inda ya fara buga wa Najeriya ƙwallo a shekarar 2022.
Yana cikin wasan Najeriya da suka wakilci ƙasar a gasar cin kofin Afirka ta 2023, wadda ƙasar Ivory Coast ta doke ta a wasan ƙarshe.
Zuwa yanzu ya wakilci Najeriya sau 27, kuma ya ci ƙwallo 8, sannan ya lambar ta MON.
Ƙungiyarsa ta Atalanta ce ta lashe gasar Europa ta shekarar 2023-2024, inda ya zura ƙwallo uku rigis a ragar ƙungiyar Bayer Leverkusen a wasan ƙarshe, domin taimakawa ƙungiyarsa lashe gasar.