AFCON 2023: Najeriya ta tsallaka zuwa wasa na kusa da na karshe

Spread the love

Najeriya ta samu damar tsallakawa zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin kasashen Afirka, bayan samun nasara a kan kasar Angola da ci 1 – 0 a wasan da suka buga da yammacin ranar Juma’a.

Dan wasan Najeriya na gaba, Ademola Lookman ne ya samu damar zura kwallon daya tilo a ragar Angola, a minti na 41da fara wasan.

Yanzu da wannan nasarar Super Eagles ita ce kasa ta farko da ta samu tikitin kai wa wasan na kusa da na karshe.

Najeriyar za ta fafata da Afirka ta Kudu ko Caper Verde wadanda za su buga wasan dab da na kusa da na karshe ranar Asabar.

Wannan ne karo na 20 da Najeriya ke halartar gasar a tsawon shekaru 34 da aka yi ana gasar ta cin kofin kasashen nahiyar Afirka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *