Fitaccen ɗan jaridar nan da ya ƙware wajen karanta littattafan adabin Hausa a gidajen rediyo, Ahmad Isa Koko ya rasu.
Wasu daga cikin abokan aikinsa – da suka tabbatar wa BBC labarin rasuwar – sun ce marigayin ya yi fama da doguwar jinya, kafin rasuwarsa yau a birnin Legas da ke kudancin ƙasar.
Ahmad Isa ya kasance ma’aikaci a gidan rediyon muryar Najeriya da aka fi sani da VON.
Marigayin ya yi fice a wani shirinsa mai suna ‘Rai Dangin Goro’ da yake gabatarwa a wasu gidajen rediyo, musamman a Kano.