AIG Umar Sanda ya jinjinawa kwamitin PCRC na jahar Kano

Spread the love

Kwamitin kyautata alakar yan sanda da al’umma (PCRC) reshen jahar Kano, ya gabatar da taron kaddamar da Calendar karon farko domin tunawa da masharuran mutanen da suka jajirce wajen taimaka wa jami’an yan sanda don tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

Shugaban kungiyar kyautata alakar yan sanda da al’umma, Alhaji Ali Hassan T. Bayero, ya bayyana cewa, Calendar da aka kaddamar ta kunshi muhimman mutane tun daga shugabannin siyasa, Sarakuna, kungiyo, shugabannin PCRC na ofishohin Yan sanda 78, da area command 11, da kuma masu gyara motocin jami’an yan sanda da wadanda suke siya mu su sababbi.

” Abunda ya sa na fadi wannan shi ne saboda tarihi, don tarihi duk Wanda ya bude Calender ba zai manta ba” Ali Hassan T. Bayero”.

Haka zalika ya ya Bawa Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, da kuma Kakakin rundunar yan sandan jahar SP, Abdullahi Haruna Kiyawa, kan yadda suke bayar da goyon baya da shi kansa AIG Umar Sanda da kuma sifeton yan sandan Nigeria, IGP Kayode Adeolu Abegketun.

Ya Kara da cewa Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini, ya sadaukar da kansa wajen Kare rayukan al’umma da dukiyoyin su.

Saurayi Ya Kashe Kawunsa Da Bindigar Kakansa A Bayelsa

Jamiā€™an Civil Defence sun cafke Dattijo mai shekaru 85 kan zargin yin garkuwa da yaro a Kano

Ali T. Bayero ya ce , CP Gumel ya shi ne Wanda jagoranci dakile kwacen wayoyin al’umma da aiyukan Daba a birnin Kano.


Da yake gabatar sa nasa jawabin Kwamishinan yan sandan Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya godewa yan kwamitin tsaron na PCRC, bisa yadda suke ba su hadin kai a koda yaushe.

CP Gumel, ya ce kwamitin kyautata alakar yan sanda da al’umma kwalliya tana biyan kudin Sabulu, kan abunda ya shafi taimaka wa yan sanda ta bangarori daban-daban.


Mataimakin Babban sufeton yan sandan Nigeria mai kula da shiya ta daya AIG Umar Muhammed Sanda, ya bukaci al’umma da su dinga taimaka wa jami’an yan sandan da bayanan sirri, domin harkar tsaro Kowa sai ya sanya hannunsa don tabbatar da shi.

Haka zalika yaba wa kwamitin kyautata alakar yan sanda da al’umma, wajen Samar da fahimtar da juna da daidaito a tsakanin jama’a.

” idan kuna da wani abu da zai taimaka mana ku sanar da mu, domin daukar matakin da ya dace.

Ya kuma gardadi masu yunkurin aikata laifuka da cewar sun yi damar Kama su, domin ba su da wajen tsira.

Alhaji Salisu Sambo, ya Yi Kira ga iyaye da ma su ruwa da tsaki wajen Samar wa Matasa aiyukan Yi , da kuma Kara habbasar taimaka wa jami’an yan sandan wajen Gyara mu su motocin da suka lalace ko kuma siya mu su sababbi, dai dai sauransu.

Taron dai ya gudana a wajen shakatawar manyan jami’an yan sanda ( Police Officers Mess) , Wanda ya samu halattar , Yan kasuwa , yan siyasa, jami’an tsaro , sarakuna, Malamai da sauran al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *