Aiki ya samu Atiku Abubakar – Fadar shugaban Najeriya

Spread the love

Fadar shugaban kasan Najeriya ta mayar wa da dan takarar shugaban kasar a jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar martani cewa yanzu ya samu abin yi da zai sanya shi ya rinka motsawa tunda ya gaza cimma burinsa na zamowa shugaban Najeriya.

A wata sanarwa, mai taimaka wa shugaba Tinubu, Bayo Onanuga ya ce Atiku Abubakar na ta koarin mayar da kansa madugun adawa ga shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa.

Sai dai sanarwar ta ce Atiku Abubakar ya gaza a sukan da yake yi wa gwamnatin saboda irin yadda kalaman nasa dangane da tattalin arziki suke kama da na irin maganganun da ake yi a teburin mai shayi.

Atiku Abubakar dai ya soki shugaba Tinubu ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi inda ya nuna cewa Tinubu ba zai iya jagoranci ba kuma yana bukatar taimako musamman dangane da abin da ya shafi tattalin arziki.

Yadda mazauna birnin Minna ke zanga-zangar tsadar rayuwa

Atiku kuma alakanta duk wahalhalu da matsin rayuwar da ‘yan kasar ke fama da su ga irin matakan tattalin arzikin da gwamnatin ta Tinubu ta dauka da suka hada da karya darajar naira.

To sai da mista Bayo Onanuga ya ce “Atiku ba zai zuga ‘yan Najeriya ba ” kasancewar da ma can shugaba Tinubu ya sanar da su cewa wasu daga cikin matakan da gwamnatin ta dauka ka iya haifar da rashin jin dadi na dan wani lokaci.

Daga karshen sanarwa ta kara da cewa “Atiku ba zai iya dakatar da ayyukan gyara da gina kasa da gwamnatin shugaba Tinubu ta sanya a gaba ba”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *