Akpabio da Natasha: Ku yi hankali kada kimar majalisa ta zube- Saraki

Spread the love

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya yi kira ga dukkan ɓangarorin shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti da su iya bakinsu domin kare martabar majalisar.

A baya-bayan nan dai shugaban Majalisar Dattawan Sanata Godswill Akpabio ya riƙa samun saɓani da Sanata Natasha, lamarin da ya sa har Natasha ta shigar da shi ƙara a gaban kotu, kan zargin ɓata mata suna.

To sai dai tsohon Shugaan Majalisar Saraki Sanata Saraki ya ja kunne duka ɓangarorin don kauce wa zubar wa majalisar kima.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa Facebook, Saraki ya ce abin da ya farun bai kamata ba, “wannan ya sa nake ganin ɓangarorin biyu da magoya bayansu na cikin majalisa da wajenta kowa ya iya bakinsa, kowa ya san tasirin da abin da yake aikatawa ko ya faɗa zai iya yi ga majalisar domin kare daraja da ƙimar da majalisa take da ita.”

Ya ce ya zama dole a bi dokar kundin tsarin mulki da dokokin majalisa wajen kawo ƙarshen wannan taƙaddama da ke tsakanin mutanen biyu.

“Sannan a yi komai a buɗe, ba tare da ba wa wani ɓangare fifiko ba. Abin da ya kamata a saka a gaba shi ne fito da gaskiya da kuma kare mutuncin majalisa wadda ita ce take da alhakin yin doka a ƙasa, saboda haka tana buƙatar a yi ƙoƙarin ba ta kariya da fito da mutuncinta.”

Ya ce a lokacin da yake shugaban majalisar, wani sanata ya zarge shi da fasaƙwaurin mota, “wanda hakan ya sa aka kafa kwamiti kuma a gaban ƴan jarida na kare kaina a gaban kwamitin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *