Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya ja kunnen “ministocinsa masu taurin kai” waɗanda ba sa amsa gayyatar majalisar dokoki.
Akpabio ya ce bai kamata irin waɗannan ministocin su samu gurbi a gwamnatinsa ba.
Akpabio ya bayyana haka ne a ranar Laraba, a lokacin da shugaban ƙasar yake gabatar da kasafin kuɗin 2025.
“Waɗanda suke ƙin amsa gayyatar majalisar dokoki ba ƴansiyasa ba ne, don haka bai kamata su samu gurbi a gwamnatinka ba,” kamar yadda Akpabio ya bayyana wa Tinubu.
- Dangote Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa N899 Kan Kowace Lita
- Yan Sanda Sun Mayar Da Baburin Adaidaita Sahun Da Aka Sace Tare Da Kama Wadanda Ake Zargi A Kano.