Akwai masu daukar nauyin zanga-zanga daga kasashen waje – Immigration

Spread the love

Hukumar shige da fice ta Najeriya, ta ce wasu ‘yan kasar da ke kasashen waje ne ke daukar nauyin masu dinka tutocin wasu kasashe a lokacin zanga-zangar matsin rayuwa.

Shugabar hukumar Kemi Nandap,ce ta bayyana haka a wajen taron manema labarai da manyan jami’an tsaron kasar suka gudanar a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Ms Kemi Nandap, ta ce suna sa ido inda da zarar wadanda ake zargin sun shigo Najeriya za su damke su.

An dai ga ɗaruruwan masu zanga-zanga yawanci daga arewacin Najeriya na rike da tutar Rasha.

Ba a san dalilin kawo Rasha cikin zanga-zangar ba, to amma ana fargabar za a iya bai wa lamarin wata fassara ta daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *