Al’ajabi: Wani mutum dan kasar Ruwanda ya killace kansa shekaru 55 saboda tsoron mata.

Spread the love

 

Wani mutum mai suna , Callixte Nzamwita, mai shekaru 71 a duniya dan asalin kasar Ruwanda, ya killace kansa tsawon shekaru 55 saboda tsananin tsoron mata.

Nzamwita, ya fara killace kansa ne tun yana da shekaru 16, a gidansa kamar yadda Idongari.ng ya ruwaito.

Rahotanni na cewa shi ne yake girka abincin da yake ci, a cikin wani daki da ya yi da itace sannan ya yi shinge dan kar ya fito waje ya ga mata saboda tsoron su.


Ma su irin wannan hali na nuna tsoro ko firgita na faruwa sakamakon Gynophobi ko kuma Phobia amma ba a tabbatar da cewar cuta ce ta tabin hankali ba.

A wani faifen bidiyo da idongari.ng, ya fassara Mista Nzamwita, ya bayyana cewa ” ya kulle kansa ne a cikin gidansa don kar mata su matso kusa dashi, kuma kwata-kwata baya son ya kusance su.

Ya kara da cewa a kwai wasu makotansa da suke taimaka masa da kayayyaki , amma suma daga nesa yake karbar abubuwan da suka kawo masa saboda bai yadda su kusance shi ba.


To sai dai abun mamaki shi ne yadda wata makociyarsa ” ta shaida cewa su ne suke taimaka masa da abinci da sauran kayan bukatun yau da kullum, duk da cewar ya kebe kansa saboda tsaron matan.


Wani mutum ya ce a lokacin da suka yi kokarin taimaka masa ya hana su kusantarsa don su yi magana da shi.
Sai dai ya ce suna kai masa kayan abinci gidan sa ,inda yake fito wa ya karba amma daga nesa.

Alamun Gynophobia na iya zama cutar tabin kwakwalwa da tsoron mata da kan sanya damuwa har ya haifar da matsala ga mai irin halin .

Masu fama da irin wannan yanayi na phobia , kan shiga damuwa a duk lokacin da suka yi ido biyu da mata, harma su kan firgita tare da yin zufa saboda tsaro.

Abun tausaya wa ne ga mutane dake cikin wannan hali na tsoron mata saboda kadai ci da firgici.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *