Alamu Sun bayyana Yadda Wasu Yan Takarar Shugabancin Kananan Hukumomi Da KansiloliN Kano Ke Shan Kwaya: NDLEA

Spread the love

Hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, reshen jahar Kano, ta bayyana cewa daga ranar 4 ga watan Satumba zuwa 9 ga watan satumba 2024, ta tantance yan karar neman shugabancin kananan hukumomi da kansiloli 289 don tabbatar da cewar basa ta’ammali da miyagun kwayoyin.

Babban kwamandan hukumar NDLEA reshen jahar Kano Abubakar Idris Ahmed, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai.

Ya ce cikin wadanda suka tantance din an samu kusan mutane 20 da suke da alamun ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Sai dai ya kara da cewa daman ka’ida ce ta gindaya hakan ga dukkan wanda yake son tsayawa takarar shugabancin karamar hukumar ko kuma kansiloli,wajibi ne a tantance su.

Kwamandan NDLEA ya ce ba a samu mace ko daya baya ba, da alamun shan miyagun kwayoyin, wanda hukumar zaben reshen jahar Kano KANSIEC ta sanya  26 ga watan oktaba 2024 a matsayin ranar zaben shugabannin kananan hukumomin jahar 44 da kuma kansiloli 484.

Wasu daga cikin wadanda aka tantance din sun bayyana farin cikin su tare da cewa, daman su yaki suke yi da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *