Sanata mai wakiltar mazaɓar Abia ta arewa a majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce albashin naira miliyan 14 yake karɓa duk wata a matsayinsa na sanata a Najeriya.
Sanatan ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na tashar talabijin na Channels na yau Alhamis.
“Ana biyana albashin naira miliyan 14 ne duk wata, kuma wannan ya ƙunshi komai da komai ne.”
Sanatan ya bayyana hakan ne domin mayar da martani ga waɗanda suke ganin albashin sanatocin ya wuce misali.