ALGION Ta Girmama Gwamna Abba Kabir Yusif Bisa Sauye-sauyen Da Ya Kawo A Fannin Yaɗa Labarai

Spread the love

Ƙungiyar Ma’aikatan Yaɗa Labarai na Ƙananan Hukumomi ta Najeriya (ALGION) ta karrama Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif, da lambar yabo ta musamman bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa harkar yada labarai da ingan tsarin gudanar da mulki a matakin ƙasa.

An mika lambar yabon ne a babban taron shekara-shekara na ƙungiyar da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba, 24 ga Satumba, 2025, inda wakilai daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya suka halarta domin tattaunawa kan ci gaban fannin yada labarai.

Shugaban ƙungiyar ALGION a matakin ƙasa, Kwamared Jibril Aliyu Bisallah, ya bayyana cewa an zaɓi Gwamna Abba Kabir Yusif ne saboda irin sauye-sauyen da gwamnatinsa ke kawo wa a fannin yada labarai, musamman a matakin ƙananan hukumomi. “Mun ga sauye-sauyen da ba a taɓa gani ba a tsarin gudanar da yada labarai a Jihar Kano tun bayan hawansa mulki karkashin jam’iyyar NNPP. Shirye-shiryen sun haɗa da ci gaba da horas da ma’aikata, haɗa su da ƙungiyoyin ƙwararru, samar da yanayin aiki mai kyau da kuma kayan aiki na zamani,” in ji Bisallah.

Bisallah ya ƙara da cewa, ba wai kawai a fannin yada labarai gwamnati ta nuna ƙwarewa ba, har ma ta sauya rayuwar al’umma ta hanyar manyan ayyuka da suka haɗa da gina sabbin tituna, gyaran makarantu da asibitoci, ƙirƙirar gadoji da sauran muhimman gine-gine a faɗin jihar.

 

Da Yake karɓar lambar yabon a madadin Gwamnan Kano, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana godiyarsa ga ƙungiyar bisa wannan karramawa da ya ce an bayar bisa cancanta da gaskiya.

“Wannan karramawar tana ƙara mana ƙaimi wajen ci gaba da ɗaukar matakai masu muhimmanci don ƙarfafa harkokin yada labarai a matakai daban-daban, da kuma tabbatar da cewa ma’aikata suna da ilimi, ƙwarewa da kayan aiki da suka dace don gudanar da aikinsu cikin nasara,” in ji Waiya.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *