Zauren Jami’an Yada Labarai na Ƙananan Hukumomi ta Najeriya (ALGION) ta kammala taronta na kasa na shekarar 2025 cikin yanayin lumana da haɗin kai.
Zauren ya mika godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa tallafawa jami’an bayar da bayanai na ƙananan hukumomi 44 daga Kano domin halartar wannan muhimmin taro.
Gwagwarmayarsa wajen inganta harkokin bayanai a matakin tushe abin koyi ne. Muna roƙon Allah Ya kara ɗaukaka shi a shugabanci da hidima.
Haka kuma, Zauren ya yaba da rawar gani da Kwamishinan Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ƙaninsa Ibrahim Abdullahi Waiya, ya taka wajen tabbatar da halartar duka mambobin Kano a taron.
Taron ya ƙunshi tattaunawa da horo kan yadda jami’an bayar da bayanai za su ƙara inganta wayar da kan jama’a game da ayyukan ci gaban gwamnati da manufofin da suka shafi al’umma.
Haka zalika, Zauren ya nuna gamsuwa da jagoranci da tallafi daga Daraktan Faɗakar da Jama’a, Alhaji Idris Zaura, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar taron.
Baya ga haka, ALGION ta yaba da jajircewa da ƙoƙarin shugabannin Zauren reshen Kano wajen ganin an gudanar da taron cikin nasara.
Sa hannu:
Abdu Bako Abdullahi, ANIPR
Mataimakin Sakataren Jiha, ALGION
Amadadin: Shugaban Zauren na Jihar Kano, Kwamarad Jamilu Mustapha Yakasai, ANIPR.